Watanni 7 Na Sanata Lamido: Mun Gamsu da aiyukkan cigaban da ya samar----Auwal Nasir 

Watanni 7 Na Sanata Lamido: Mun Gamsu da aiyukkan cigaban da ya samar----Auwal Nasir 
Mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai na Sanata Ibrahim Lamido waton Alhaji Auwal Nasir ya bayyana gamsuwarsa da ta al'ummar gabascin Sakkwato kan dimbin aiyukkan da ya samar a cikin wata 7.
Alhaji Auwal ya ce Sanata Lamido yana gudanar da wakilcinsa ne cikin tsoron Allah da kokarin ciyar da jama'a gaba, hakan ne ya sanya ya samu gagarumar nasara a cikin kankanen lokaci in da  ya samar da aiyukkan cigaba masu yawa.
Auwal ya zayyano kadan daga cikin aiyukkan cigaba da aka yi.
 "Lamido ya biyawa Dalibai na Jami'ar Usman Danfodiyo rabin kudin makaranta 'yan asalin yankinsa na Sakkwato ta Gabas kimanin 10300.
 "Lamido ya dauki nauyin karatun matasa 'yan Asalin yankinsa zuwa Jami'ar North West dake sokoto kimanin Dalibi 10.
"Lamido ya dauki nauyin sanyawa kananan Hukumomin yankinsa soler a garuruwan Achida  dake karamar hukumar mulkin Wurno dakuma Rimawa a karamar hukumar mulkin Goronyo da sauran sassan Gabaschin Sakkwato," kalaman Auwal Nasir.
Ya cigaba da jero hobbasar Sanata Lamido ya ce "kokarinsa na tallafawa dalibai ya baiwa dalibai kimanin 5800 kowanensu naira dubu 50 don ganin an saukaka masu karatu a cikin halin da ake ciki.
 "Lamido ya gina cibiyar koyon na'ura mai kwakwalwa a kananan hukumomin  Illela da Gwadabawa inda yanzu aikin na cigaba a sauran kananan hukumomin yankinsa.
"Bangaren samar da Ruwan sha Sanata Ibrahim Lamido na cigaba gina Rijiyoyin Ruwa masu aiki da hasken Rana a kananan hukumomin  yankinsa guda Takwas.
"Saramar da aikin yi ga matasa Sanata Ibrahim Lamido ya sanya matasan yankinsa aikin tsaro na farin kaya (civil Defense) kimanin matashi 11 dukkaninsu a Gabascin Sakkwato suke.
 "Sanata Ibrahim Lamido ya tura sunayen matasa zuwa ma'aikatar kiwon lafiya dake Babban birnin tarayya kimanin matashi 30 Insha Allahu kuma za su ji albishir Daga yanzu zuwa kowane lokacin da kake karanta rubutun nan.
Babban gefen da yafi muhimmanci a wurin Sanata fannin samar da tsaro  ya dauki nauyin gyaran Babbar motar Jami'an tsaro tare da daukar nauyin baiwa Jami'an alawus a kowane karshen wata," tsakure daga cikin aiyukkan Sanata Lamido.