APC Na Yunkurin Hana Sanatoci Da 'Yan Majalisar Wakillai Kada Kuri'a A Zaben Shugaban Kasa

APC Na Yunkurin Hana Sanatoci Da 'Yan Majalisar Wakillai Kada Kuri'a A Zaben Shugaban Kasa

Sabon rikici ya kunno kai a babbar jam'iya mai mulki ta APC kan wani shiri na hana sanatoci da 'yan wakillai da ba su rike da mukami a majalisar tarayya kada kuri'a wurin zabar shuguban kasa a zaben fitar da gwani na jam'iyya.

A yanzu yanda kudin dokar jam'iyyar ya tanadar dukkan mamba a majalisar tarayya tsoho da wanda yake sama yana da damar jefa kuri'a a zaben fitar da gwani na shugaban kasa, amma ana son yiwa dokar gyaran fuska domin a cire su.

Sashe na 12.1 a kundin dokar APC ya ce mambobi a majalisar tarayya da mambobin kwamitin amintattu da shugaban jam'iya na kasa da majalisar zartawarwa jam'iya gaba daya da Shugaban kasa da mataimakansu tsoffi da masu ci da gwamnoni da mataimakansu da suke cikin jam'iyar dukkansu za su kada kuri'a a zaben fitar da dan takarar shugaban kasa. 

Sauran masu shiga zabe 'yan majalisar tarayya tsoffi da shugabani  majalisar dokokin jiha da mataimakansu da masu rike da mukamai da dukkan mamba a majalisar wanda yake a jam'iya, sai shugabannin jam'iyya a jihohi da majalisar zartawarsu.

A gyaran kundin tsarin da jam'iyar za ta yi tana son kawai shugabanni a majalisar tarayya ne kawai za su yi zabe, saura 'yan majalisa su tsaya gida su kalla a tv.

Sakataren jam'iya na kasa ya ce wannan kudiri ne kawai kowa nada damar sanya tunaninsa na gyara kafin a tabbatar doka ta karshe da za ayi amfani da ita.