YANDA AKE HAƊA PIZZA NA ALFARMA

YANDA AKE HAƊA PIZZA NA ALFARMA

GIRKI ADON MACE

YANDA AKE HAƊA PIZZA
Abubuwan hadawa (dough)

Filawa kofi daya
Yeast cokali daya
Bakar foda (baking powder) cokali daya
Man zaitun ko man gyada cokali uku
Dan suga da dan gishiri kadan
Yadda ake hadawa (dough)

Ki hada filawa da duk abubuwan da muka lissafa a sama sai ki dama su da ruwa, kwabin ya yi tauri ba ruwa ruwa ba.
Ki dama ya hade sosai sannan ki buga shi ya bugu da kyau. Sai ki rufe ki ajiye a rana ko wuri mai dumi din ya taso. Kafinnan sai ki shiga hadin sauce dinsa.
Sauce
Souce ɗin pizza kala kala ne, amma yau za mu yi na beef ne (jan nama).

Abubuwan hadawa (sauce)

Albasa
Tattasai
Attargu
Tumatirin Leda ko ketchup
Nama mara kasha
Karas
Koriyar wake (green beans)
Koriyar tattasai
Masaran gwangwani (sweet corn)
Sai kuma za a buqaci cheese (jubna)
Yadda ake hadawa (sauce da pizza)

Ki yanka nama kanana, bayan kin wanke ki sulala ya tsotse ruwan jikin sa tsaf da kayan qanshi.
Sai ki soya albasa ki kawo tumatir na leda ko ketchup ki zuba, sannan ki kawo jajjagen tarugu da tattasai ki zuba, ki kawo naman ki zuba, sai kuma ki sa maggi da dan ruwa ki bari ya tsotse ya yi kauri.  Sai ki ajiye a gefe.
Yanzu lokaci ya yi da zaki duba kwabin filawan ko ya taso.
In ya taso da kyau. Sai ki dauko abin murza filawa (chopping board) ki bubbuda filawan nan (rolling) ya yi round kamar fai fai.
Sai ki samo tirai din obin (oven) ki jera su a kai yadda baza su takure juna ba.
Sai ki debo sauce dinki, ki zuba a saman filawarki mai kamar fai fannan.
Sai ki kawo karas  da koriyan tattasai da koriyan wake da masaran ki watsa su a kai sannan ki kawo cheese(jubna) ki zuba a karshe.In kinyi haka sai ki gasa a oven dinki sama da qasa su gasu.  
Hmmmm wani abin sai an dandana

By Zainab Muhammad (Indian girl)