Yadda Ake Haɗa SAMOSA Na Alfarma
BASAKKWACE'Z KITCHEN
KAYAN HADI
filawa kofi 2
Ƙwai 2
butter spoon 1
Baking powde spoon1
albasa 2
nama kofi 1
maggi
gishiri
curry
mai
spices
YADDA ZAKI HAƊA
Aunty na ki soya niƙaƙƙen nama Sama sama tareda albasa, saiki sa maggi da gishiri da curry da spices.
Ki tankaɗe filawa kisa baking powder butter ƙwai gishiri saiki kwaɓa ki muraza tai laushi sai a yanka ta ƙanana kowane amurzashi har yayi fele fele, sai ki zuba sai a zuba spoon 1 na haɗin nama ciki alinka gefe biyun yadda ake naɗata. Sai a datseta gefe gefen sai a soya.
Kuma kina iya yanka kabeji albasa agurza Kara's a soya Sama sama a haɗa da nama. Kuma ana kwaɓa filawa da ruwa kamar kwabin spring roll idan an gasa a soya a mai.
NOT
Aunty na kina iya na zallan kabeji da karas da albasa da tattasai da tarugu,in baki da halin nama
MRS BASAKKWACE
managarciya