'Yan ta’adda sun kashe shugaban riƙo na Miyetti Allah tare da yin garkuwa da matansa da ‘yar sa
Ana zargin ƴan ta'adda sun kashe shugaban rikon kwarya na Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah a Jihar Katsina, Alhaji Amadu Surajo.
Haka kuma, sun kashe wasu mutane uku, sun jikkata mutane da dama.
Guardian ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a jjiya Asabar zuwa safiyar Lahadi, lokacin da ƴan ta'addan su ka kai hari kauyen Mai Rana da ke Karamar Hukumar Kusada.
An rawaito cewa ƴan ta'addan sun yi garkuwa da matansa guda biyu tare da ‘yar sa, wacce ke karatu a daya daga cikin jami’o’in gwamnati a kasar.
Sai dai wata majiya ta ce an sako matar farko ta Surajo daga hannun 'yan ta'addan.
managarciya