An kama Tsoho Mai Shekaru 59 Da Yayiwa Jaririyar Makwabcinsa 'Yar Wata 18 Fyade A Bauchi

An kama Tsoho Mai Shekaru 59 Da Yayiwa Jaririyar Makwabcinsa 'Yar Wata 18 Fyade A Bauchi
 
Daga Nas Das Bashir.
 
Rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta kama wani mutum mai shekaru 59 da laifin yiwa jaririyar makwabcinsa ‘yar watanni 18 fyade.
 
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Ahmed Wakil, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga Yola 24 a jiya Asabar, 13 ga watan Agusta, ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan mahaifiyar jaririn mai suna Nenkat Danladi ta kai karar ofishin ‘yan sanda na Yelwa lamarin fyaden.
 
“A ranar 09/08/2022 da misalin karfe tara Tara na dare, wata Nenkat Danladi ‘ mai shekara 31 a Yelwan Kagadama ta kai kara ofishin ‘yan sanda na Yelwa cewa a ranar 06/08/2022 da misalin karfe 11:30 na safe ta hadu da wani Alhamdu Yusuf, mai shekaru 59. a kan gadonta tare da diyarta Blessing (ba sunan gaskiya ba) da jini jinajina a al’aurar ‘yar ta na ta zubar da jini.
 
Matar nan da Nan ta garzaya da yarinyar  zuwa Asibitin Koyarwa na ATBU Bauchi domin duba lafiyarta, kafin ta shigar da Kara.