Gidauniyar Bafarawa ta Kammala aikin  rabon Abinci  a kananan Hukumomin  Sokoto 

Gidauniyar Bafarawa ta Kammala aikin  rabon Abinci  a kananan Hukumomin  Sokoto 

 Daga Mukhtar A Haliru Tambuwal Sokoto.

Kwamitin "Aikin Maida Alkhairi da Alkhairi "   wanda Maigirma Sadaukin Sakkwato Malam Muhammad Lawal Maidoki ke Jagoranci da Wasu Mambobi 7 , karkashin Gidauniyar Attahiru Bafarawa Foundation, sun samu Nasarar kammala, Aikin Rabon Tallafin Abinci a daukacin Kananin hukumomin Jihar Sokoto, cikin Nasara. Kwamitin Wanda ya tsara Wasu Muhimman Ayukkan Alkhairi da zaayiwa Alummar Jihar Sokoto, Musamman mabukata,Yangudun hijira, Masu lalura ta Musamman,Yara Marayu,Uwayen Marayu,Masu rashin lafiyar tabin hankali,tsofaffi,limamamai da sauran su. Kwamitin Wanda ya soma Rabon Abinci ga Yangudun hijira da ke Kananin hukumomi Ukku  inda aka Raba Masu kusan Buhuhuwan Abinci Guda Dari Tara (900) da kudi Naira Miliyan  Tara (#9,000,000:00) Yayin da Kananin Hukumomi Ashiri aka baiwa kowacen su Buhuhuwa Dari (100) da kudi Naira Miliyan Daya da Dubu hamsin (#1,050,000:00.) Shugaban Kwamitin Malam Muhammad Lawal Maidoki yayi Kira ga wadanda suka amfana da Kada suci su kadai Suma su Tallafawa mabukata na tare da su, yayi kira da ayiwa Wanda ya bada Tallafin Addua Allah ya biya shi ,ya kuma yi Kira ga Alumma da A fitar da Zakka ko abada Wakafi kamar irin wannan da Garkuwa Sakkwato Yayi , yayi Godiya ga Gwamnatin Jiha da Majalisar Sarkin Musulmi da uwayen kasa da kananin hukumomin kan goyon bayan da suka Bada na Samun Nasarar Shirin.Sakataren Kwamitin Alh Sagir Attahiru Bafarawa ya bayyanawa Manema labarai Jin kadan da Kammala Rabon,  cewa shirin baida Alaka da siyasa ko bangaranci anyi ne domin kawo dauki na matsin da Alumma suke ciki Maimakon barin Gwamnatin kadai da Dawaiyar. Wasu Shugabannin Kananin hukumomi da Uwayen kasa da Shugabannin Kananin kwamitocin  sunyi yabawa Tsohon gwamnan Kan wannan Aikin da kuma Kira ga sauran Yan siyasa da Masu sukuni da suyi irin wannan Aikin dan Kara tallawa Alummar su. Sarkin Malamman Sakkwato , Sheikh Umar na Malam Boyi, yayi Nasihohi akan Muhimmancin Fitar da Zakka da Bada Sadaka, da neman Ilimi da Taimakawa Alumma. Malam Kabiru Shehu Binji,Alh Nasiru Bafarawa,Alh Ahmad Gyarafshi,Prof.Malami Umar Tambuwal sun yi Karin haske akan Dinbin Ayukkan da Zaa aiwayar a nan gaba. Wasu bayin Allah da suka Amfana sunyi Godiya da Addua ga Tsohon gwamnan, da Yan Kwamitin da duk Masu hannu cikin Wannan Aikin Alkhairin .