'Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojojin Najeriya Kwantan Ɓauna, Sun Kashe Wasu a Zamfara

'Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojojin Najeriya Kwantan Ɓauna, Sun Kashe Wasu a Zamfara

Sojoji uku sun rasa rayukansu yayin da wani ɗaya ya jikkata bayan wasu tsagerun 'yan bindiga sun musu kwantan ɓauna a kusa da ƙauyen Dolen-Kaura, ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda, jihar Zamfara. Wani ɗan asalin yankin wanda ya roki kar a saka sunansa, ya shaida wa jaridar Punch cewa lamarin ya faru ne ranar Laraba da daddare lokacin da yan ta'adda suka mamayi motar sojojin da ke bakin aiki. 

A cewarsa, sojojin sun samu bayanin cewa wasu 'yan ta'adda sun shirya zasu kai hari ƙauyen Kada-Mutsa, ƙaramar hukumar Zurmi, bisa haka aka tura su daƙile kai harin, jaridar Sahara Reporters ta ruwaito. Bisa rashin sa'a, yan bindigan dajin suka sami labarin cewa sojoji na kan hanya zasu kai musu samame, "Nan yan bindigan suka yi kwantan ɓauna suka buɗe wa motar da ta ɗakko sojojin wuta, uku suka mutu ɗaya ya ji rauni," inji shi.
 
Mutumin ya faɗi sunan shugaban tawagar sojojin da, "Mejo Emos," inda ya bayyana shi da gwarzon jami'in soja da bai san tsoro ba. "Gwarzon soja ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa domin kare rayukan mutane a ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda. Mamacin ya kasance ko da yaushe a shirye idan aka yi kiran gaggawa 'yan bindiga sun kai hari." 
"Mutuwara babban rashi ne ba wai ga mazauna Ƙauran Namoda da kewaye kaɗai ba, baki ɗaya al'ummar jiha sun yi rashi." Har yanzu da muke kawo muku wannan rahoton babu wata sanarwa daga hukumar soji ko ta 'yan sanda game da lamarin da ya auku.