Bankin CBN Zai Fara Cire Kudi Daga Asusun ’Yan Najeriyan da Suka Ci Bashin Gwamnati

Bankin CBN Zai Fara Cire Kudi Daga Asusun ’Yan Najeriyan da Suka Ci Bashin Gwamnati

 

Babban bankin Najeriya (CBN) ya ce zai fara zare kudade daga asusun bankin gwamnatin jihohi dana  wasu 'yan Najeriya domin warware bashin da ake binsu. 

Daraktan raya fannin kudi na CBN, Yusuf Yila ne ya bayyana hakan a Abuja a ranar Laraba 28 ga watan Satumba, The Cable ta ruwaito
Yila ya ce babban bankin ya shirya karbo kudade daga gwamnati jihohi da manoma ne da suka ci gajiyar kowane daga shirye-shiryen rance na gwamnati tarayya. 
Duk da cewa bai ambaci jihohin da ake bi bashin ba, Yila ya ce babban bankin kasa ta hannun asusun rarraba kudaden jihohi na FAAC ya fara ciran kudaden da ake bin jihohin a kowane wata.
A cewarsa, wanda suka ci bashin CBN a karkashin shirin noma na ABP da CAC na daga cikin wadanda shirin zai shafa 
"Kowane mutum ko jihar da ta karbin rancen ABP za ta biya. Muna da BVN dinsu. 
"Wadannan mutanen kananan manoma ne da suka karbi kudi domin noma daga gwamnatin jihohi karkashin AVP, amma har yanzu basu biya ba." 
Hakazalika, ya ce CBN ya fara magana da hukumar  Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) magana wajen tabbatar da dawo da kudaden rancen a lokacin da aka shata.