Lamido Ya Yi Ta'aziyar Mutanen Da 'Yan Bindiga Suka Kashe A  Sabon Birni 

Lamido Ya Yi Ta'aziyar Mutanen Da 'Yan Bindiga Suka Kashe A  Sabon Birni 

 

Dan takarar Sanata a yankin Sakkwato ta Gabas a jam'iyar APC Alhaji Ibrahim Lamido ya yi ta'aziyar mutanen da 'yan bindiga suka kashe a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sakkwato.

Lamido a sakonsa ga manema labarai ya yi tir da aiyukkan 'yan bindiga a yankin Sakkwato ta Gabas, in da suka sanya mutane cikin halin kunci da wahala kan wata bukata ta su da ta sabawa Allah da manzonsa.

Dan takarar ya daura laifin sakacin lamarin da aka kasa magance shi tsawon lokaci hannun mahukunta da gwamnati domin ita ke da wuka da nama kan kare rayuwa da dukiyoyin al'ummar Sakkwato, 'ba wani dalili da zai sanya a rungume hannu ana kallon mahara na cin karensu ba babbaka a yankin da ke da yawan al'umma da kasar noma da ilmi sai dai kawai in ba a damu da cigaban jiha ba ne, wanda ba za mu lamunce hakan ba in Allah ya ba mu damar wakilcin jama'a dole ne a samar da bakin zaren magance tayar da hankalin jama'a, ba da hakki ba', a cewarsa.
Lamido a cikin takaici bayan da 'yan bindiga suka kashe mutane 11 a cikin kwana biyu a Sabon Birni suka hana fita ko shiga Sabon Birni daga Sakkwato ya gabatar da ta'aziyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayuwarsu, ya kuma roki Allah ya kubutar da wadanda ke hannun 'yan bindigar cikin koshin lafiya.

Ya ba da tabbacin cigaba da ba da tasa gudunmuwa na abin da yake iyawa don samar da sassaucin matsalar tsaron da ke addabar yankinsu da jiha baki daya.