Tinubu: Babu Cire Tallafin Mai a Jawabin Ranar Rantsuwa Amma Na Sanar da Cire Wa

Tinubu: Babu Cire Tallafin Mai a Jawabin Ranar Rantsuwa Amma Na Sanar da Cire Wa

 

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana tallafin man fetur da gwamnatin Najeriya ta jima tana biya a matsayin 'Damfara' kuma mai daƙushe ci gaban ƙasa. 

Channels tv ta rahoto shugaban ƙasar na cewa tallafin na ƙara tallafawa 'yan fasa kwauri da kuma rage wa wasu ƙasahen Afirka wahalhalu da tashin farashi. 
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne yayin ganawa da mutanen Najeriya da ke rayuwa a ƙasar Faransa da wasu ƙasashe a nahiyar Turai. 
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Dele Alake, shi ne ya bayyana kalaman da Tinubu ya faɗa a wata sanarwa da ya fitar. 
Shugaba Tinubu ya yi bayanin cewa masu ba shi shawara ta musamman, Wale Edun, da Dele Alake, ba su sanya batun cire tallafin man fetur ba a jawabinsa na ranar rantsuwar kama aiki. 
"Amma sai na ji a raina ya kamata na cire tallafin nan tun a rana ta farko da shiga Ofis. 
Da na hau kan munbari na ƙara samun kwarin guiwa, na ce tallafin mai ya tafi."