KPF ta dauki nauyin karatun yaron da ya kirkiro Gilashin Makafi a Kano
Daga Ibrahim Hamisu, Kano.
Kungiyar Ƴan Kishin Kano Tsantsa, wato Kano Patriotic Front (KPF) ta ci alwacin daukar nauyin cigaban da karatun yaron nan da ya kirkiri Tabarau dan jagora ga Makafi, wato Ilyasu Aminu Alkasim da aka fi sani da Khalifa Aminu,
Shugaban Kungiyar Manjo Janar Ibrahim Sani mai ritaya ne ya bayyana haka a wata ganawa da ya yi da Khalifa Aminu a ofishin kungiyar da ke kan titin Zariya da ke Kano,
Manjo Janar ya bayyana cewa irin wadannan yaran da suke da baiwar ƙirƙira kungiyar ba za ta barsu a haka ba, inda ya ce
"Za mu dauki gabarar tallafawa wannan yaron da duk abubuwan da ya ke bukata domin bunkasa fasaharsa"
"Baya ga daukar nauyin karatunsa da KPF ta yi na wannan yaron, akwai wani shiri da muke yi inda za mu gayyato dukkanin ƴan Kano masu irin wannan fasahar ta kirkira mu zauna da su don mu ga yadda za'a yi mu taimaka masu taken shirin shi ne 'NUNA MANA ABINDA KA IYA KO ZAKA IYA'. Inji Manjo Genar Ibrahim
Khalif Aminu mai shekaru 17 ya kirkiri galashin ne ta yadda idan makaho ya saka shi, da ya hangi gini ko wani abu zai nuna alama cewa akwai wani abu, don haka makaho zai iya tafiya duk inda ya ke so ya je ba tare da dan jagora ba.
An dai kafa Kungiyar KPF ne a shekarar 2024 tana da membobi fiye da 350 Babbar manufarta shi ne daukaka Kano zuwa matsayinta na babbar cibiyar zamantakewa da tattalin arziki da al'adu da masana'antu, da kuma kasuwanci a Arewa da yankin ECOWAS.
Kazalika KPF na da kwamitoci 18 da suka kware a fannoni daban-daban na rayuwa.
managarciya