Tsaro:Hakimin Paiko Ya Haramta Shagalin Bukin Hawan Dutse Da Ake   Yi Duk Ƙarshen Shekara

Tsaro:Hakimin Paiko Ya Haramta Shagalin Bukin Hawan Dutse Da Ake   Yi Duk Ƙarshen Shekara
 
 
Daga Babangida Bisallah, Minna
 
 
Hakimin Paiko  Alhaji Muhammad Mañsur Mustapha da ke masarautar minna, ya haramta hawan dutsen Paiko saboda dalilan tsaro. Kamar yadda aka saba bisa al'ada matasa kan hau dutsen duk ranakun 25 ga watan Disamba a lokacin kakar abinci dan nuna farin ciki da zuwan qarshen shekara mai qarewa.
A wata takardar da ofishin hakimin wanda shi ne Durbin masarautar Minna ta fitar, ta bayyana hawan wannan dutse ya samo asali ne tun kaka da kakanni, amma sakamakon halin da ake ciki yau na dalilan tsaro da kuma gurvacewar tarbiyar matasa sun mayar da hawa dutsen wani masomin fitina da suke tafiya da makamai dan aukawa junan su.
Gwamnati da jami'an tsaro suna bakin kokarin su na ganin an dawo da zaman lafiya a cikin al'umma, kan haka mu ka dacewar dakatar da hawan dutsen tunda bai sabawa dokokin kasa ba, bukatar mu al'umma ta zauna lafiya ayi ziyarce ziyarcen dan dangi da sauran yan uwa da cigaba da tafiyar da zumunci, yafi baiwa matasa dama suna anfani da makami dan aukawa yan uwa saboda wasu dalilan rashin tarbiya.
Da ya juya kan direbobi masu safarar jama'a zuwa wasu garuruwan saboda bukin kirismati kuwa, ya jawo hankalin su da su guji tukin ganganci da daukar fasinja fiye da kima, dan hakan kan haifar da hadurra da wani lokacin ya kan janyo rasa rayuka.
Hakimin yayi kira ga jami'an kula da hanyoyi da tukin mota da su kara kaimi wajen cafke dukkan direban da ya sabawa ka'idar tuki, saboda tsare rayukan jama'a.
Alhaji Muhammadu Mansur, yace arziki na Allah ne, kuma ita lafiya renonta ake, kar dan neman tara abin duniya yasa ka jefa rayukan jama'a cikin wani halin da zai mayar da su baya.
Hakimin ya yabawa gwamnati, da jami'an tsaro kan irin rawar da suke takawa wajen ganin an samu zaman lafiya a kasar nan, dan haka akwai bukatar jama'a su bada goyon baya wajen bin doka da oda da sanya idanu akan dukkan abinda zai janyowa zaman lafiya koma baya.