Rashin Tsaro Ya Ta'azzara Dan Majalisar Wakilai Daga Kebbi Ya Shaidawa Zauren Majalisa
Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Zuru Fakai Danko Wasagu Sakaba da ke jihar kebbi Hon Kabir Ibrahim Tukura ya gabatar da kudurinsa a majalisar wakilai kan matsalar tsaron da ya addabi mazabunsa.
Tukura ya shaidawa majalisar wakilai cewa a yankin mazabunsa ana fama da matsalar rashin tsaro inda a kullum yan bindiga ke cin karensu babu banbaka.
Hon Kabir Tukura ya tabbatar wa majalisar wakilai cewa tarin yan bindigar dake dauke da muggan makami na bi gari suna ta'addanci.
Hon Kabir Tukura ya bukaci majalisar kasar da takai daukin gaggawa ga manoma da al'ummar gari inda yanzu haka yan ta'adda ke hana ma mutane fita daga gonakinsu.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da al'ummar Zuru Fakai Danko Wasagu Sakaba musamman ma mazauna kauyuka suke fama da hare-haren yan ta'adda.
Tukura ya bukaci gwamanatin tayi duk mai yuyuwa wajen kai dauki ga mazauna kauyuka inda yanzu hakan suke kara kokawa kan karuwar hare-haren yan bindiga a yankunan.
Abbakar Aleeyu Anache
Mai ba Hon Kabir Tukura shawara na musamman kan Harkokin Yada Labarai (SA)
12th October 2023:
managarciya