Abin Da Babba Ya Hango:Fita Ta Biyar
Zuwan sa kusan uku gidan Hajiya Turai sai dai har lokacin da yayi zuwa na uku ba ita ba labarinta a ƙargame ƙofar gidan take a haka ya juya ya nufi gida, cike da tashin hankalin ina ta nufa...
ABINDA BABBA YA HANGO.......!
RUBUTAWA; DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.
بسم الله الرحمن الرحيم
Fitowa ta biyar.
Ɗakin daya kama musu ya nufa da ita kai tsaye yana faman shashafa sassan jikinta, ya yinda ita kuwa sai faman ƙara shigewa jikinsa ta ke yi.
Kallonsa ta yi da idanuwanta da suka fara canjawa cikin sarƙewar murya ta ce "Alh yaushe ka dawo?."
Janyeta daga jinsa ya yi ya hau rage kayan dake jikinsa , saida ya koma daga shi Sai 'yar ciki da three quater, kana ya zauna a gefenta yana shafar fuskarta ya ce "yanzu yanzun nan muka sauka, nasan kina nan shi'isa kai tsaye nayo nan, don kinsan na yi missing ɗinki irin sosai ɗin nan ", ya faɗa tana mai kashe mata ido ɗaya.
Haka wannan daren suka sheƙe ayarsu ba kunya balle tsoron Allah.
Ubangiji Allah ya tsare mana imanin mu, Amin ya Allah.
Gaba ɗaya hankalinsa ya gama tashi, ganin har 12am ba ita ba labarinta.
Zuwan sa kusan uku gidan Hajiya Turai sai dai har lokacin da yayi zuwa na uku ba ita ba labarinta a ƙargame ƙofar gidan take a haka ya juya ya nufi gida, cike da tashin hankalin ina ta nufa.
Gaba ɗaya ya rasa gunda zai sanya kansa, ba tada gurin zuwa sai gidan Hajiya Turai wacce ta ce masa ƙanwar mahaifiyarta ce.
Har ƙarfe 2am ba ita , kala yana kiran wayarta tana shiga har aka fara ce masa switch off.
Ƙarfe 6am ya koma jan mota ya nufi gidan Hajiya Turai, a ƙargame har yanzu garkar take.
Ya jima a wurin kana ya ja motar ya bar gurin.
Kai tsaye family hause ɗinsu ya nufa.
Sashen Hajiya Umma ya nufa hankalinsa a tashe yake sanar da'ita komai.
Ita ma jikinta ya yi sanyi sakat yau , amman ba ta nuna masa damuwarta ba ta dai ce Allah ya bayyana ta.
Ƙarfe 12pm jirgi ya lula da su cikin gajimere daga Kano zuwa Lagos ita da Alh Sambo zai halarci wani taron ƙarawa juna sani na tsawon mako biyu.
A babban hotel ɗin dake cikin birnin Lagos suka sauka, sosai yana yin garin ya tafi da imaninta.
Wannan ne karo na farko data taɓa shiga garin.
Sabon sim card ta sanya a cikin sabuwar wayar da Alh Sambo ya mallaka mata a daren jiya, don ta manta da wayarta a gurin Hajiya Turai.
Gaba ɗaya Allah ya shafe mata sanin wai ita matar aure ce, sosai suke ɓarje lokacin su ita da Alh Sambon ta, wanda ke sakar mata maƙudan kuɗaɗe ita kuwa ta buɗe jikka sai kwasar nata rabo ta ke yi.
★★★★★★
Har gurin jami'an tsaro case ɗin ɓatan ZULFA'U yakai amman har tsawon kwana uku ba ta ba labarin ta.
Duk ya fice daga hayyacinsa, ya yi baƙi ya rame sai uwar sumar daya tara a saman kansa, tunaninsa ɗaya ko a wanne hali take?.
Sosai Hajiya Umma ke kwantar masa da hankali , amman gaba ɗaya baya kamar wanda ake ƙara zautawa.
Yawo yake yi a cikin mota yana ci gaba da zagaye ciki da wajen Kano waiko Allah zai sa ya ganta, amman ko mai kama da ita bai gani ba.
A haka ya gaji ya koma gida ya zube yana mai sakarwa Hajiya Umma kuka kamar ƙaramin yaro.
Sosai hankalinta ya tashi ganin tilon ɗanta yana kuka a kan mace sai da bayadda ta iya sai addu'ar Allah ya bayyana masa matar sa ko hankalin kowa ya kwanta.
Sai da suka yi sati biyu a can Lagos kana da maraicen ranar litinin jirginsu ya sauka a filin jirgin saman malam Aminu kano.
A bakin ƙofar gidan Hajiya Turai motar Alh Sambo ta yi parking, kayan tsarabarta aka hau jibge mata , ta jima a cikin motar suna ci gaba da sharholiyarsu kana ta fito tana yauƙi tana ƙarawa ta nufi cikin gidan.
Da murna Hajiya Turai ta shiga tarbonta haɗi da ajiye mata kayan ciye ciye iri iri, tana me zama kusa da ita tana latsa fatan jikin ta.
Sai fadan ta keyi "kai lallai garin Lagos bana zan sauka, kinga yadda kika canja cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kuwa?".
Dariya suka sanya lokaci ɗaya suna taɓewa kana ta ce "Hajiya ai dole ne kinga yadda Alh. ke kula dani kuwa?, hummm ai ingaya maki abin baya ma faɗuwa sai kin gane ma idanuwanki zaki gasgata."
Sosai suka ci gaba da fira suna masu bude manya manyan jaka da Alh. Sambo ya shaƙo mata da kayan tsara ba, kama daga kayan maƙulashe har izuwa kan suturar sanyawa, uwa uba maƙudan kuɗaɗen daya ke yi mata ɓari a ko wacce safiya waɗanda bata san a dadinsu ba.
Hajiya Turai sai santin kaya ta keyi tana mai yabawa Alh. Sambo.
Ko a ranar a gidan Hajiya Turai ta kwana da zummar washe gari su bazama neman bokan da zai yi masu aiki akan Ƙasim don a kulle masa baki, a cewar ta za ta fara biyan Alh. Sambo zuwa ƙasashen duniya da yake fita yawon shakatawa.
Washe gari haka suka shirya cikin ƙasaitacciyar shiga , kana suka haye saman sabuwar motar da Alh. Sambo ya mallaka mata jiya, suka shiga cikin gari.
Sun jima suna yawon shakatawa sannan suka nufi wani ƙauye da akayi masu kwatance aikin bokan kamar yanka wuƙa yake.
Sosai suka ci tafiya sai da suka wahala sosai sannan suka isa gurin.
Daji ne sosai baka jin motsin komai sai kukan tsuntsaye yayinda bukkar bokan take a tsakiyar dajin sai uban layin da suka sama a wurin.
A haka suka yi zaman jiran layi kusan magarib suka samu layin yazo kansu.
Shiga suka yi cikin bukkar a ƙafar su sanye da talkami ɗaya-ɗaya tare da ashariya a bakinsu, wannan ita ce ƙa'idar shiga wurin bokan.
Kallonsa suka yi da niyar yi masa bayani ya dakatar da su ta hanyar ɗaga masu hannu.
Sosai suka yi mamakin jin yadda yake zayyana masu abin da ke tafe da su, har mamakin na su ya bayyana a kan fuskarsu.
Umurnin zube masa kuɗi ya basu kana ya ce "ku je yau ɗin nan za ki ga aiki da cikawa, sai yadda kika yi da shi, ko kwanciya ya yi idan baki ce tashi ba ba shi ba tashi a gurin, sai dai da sharaɗin za ki daina sallah harna tsawon makonni uku."
Cike da farin ciki ta amsa masa da angama, kana suka fito daga cikin bukkar hankalinsu kwance suka nufi gida.
A bakin ƙofar gidan Hajiya Turai ta yi parking sannan ta fita ta fito da tsarabarta ta sanya a bayan mota kana taja motar ta nufi hanyar gidanta ranta wasai da shi.
Cike da murna Ayuba ya buɗe mata get ɗin shiga gidan, yana mamakin a ransa ashe dama ba ɓata ta yi ba, bai ƙara mamaki ba sai lokacin da ya ga ta fito da jikkuna daga bayan motar tana mai kwala masa kira ya shigar mata da su.
Bayan ya gama shigar mata da komai cikin gidan, ya dawo bakin get yana neman layin uban gidansa.
Bugu ɗaya ya ɗaga wayar cikin sanyayyiyar murya yana mai amsa masa sallamar da yayi masa.
Gaya masa dawowar Hajiyar gidan yanzun nan, a matuƙar ƙiɗime ya miƙe daga kwance da yake a saman carpet ɗin Hajiya Umma, yana mai lalubar key ɗin motar.
Yana tafe yana gayawa Hajiya Umma anga ZULFA'U, cike da mamaki take binsa da kallo harya ɓacewa ganinta, addu'ar kariya ta cigaba da yi masa daga sharrin makirar matar sa.
Tafiyar 40minutes sai gashi cikin 10minutes ya isa gidan.
Ko dai daita parking ɗin motar bai yi ba ya fice da gudun tsiya ya faɗa gidan yana ƙwala mata kira, "Zuly Zuly Zuly!!!."
Turus ya yi lokacin daya ganta hakimce a saman kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya sai girgiza su take yi.
Kallonsa ta yi sheƙeƙe kana ta ce "lafiya kake kwalamin kira tun daga waje , sai kace wacce ta yi ma sata?."
Murmushin yake ya saki sannan ya ce "lafiya ƙalau kawai nayi kewarki ne."
"Okey" kawai ta ce.
Sannan ta sake kallonsa ta ce "plx dear ɗan shiga kitchin ka samar min wani abu na sanyawa cikina, Allah tun safe rabona da abinci."
Jikinsa na rawa ya nufi kitchin ɗin yana me mamakin kansa na kasa yi mata musu da ya yi.
Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ya kammala ya ɗauko ya kawo mata har Parlour, cikin jin daɗi ta hau ci tana lumshe idanuwa "ba ƙarya ya iya girki ashe", ta faɗa cikin ranta.
Tana kammalawa ta miƙe ta nufi bedroom tana bashi umurnin kamin ta fito daga cikin ɗaki ya kankanta Parlourn ya yi shara da morping.
Jikinsa har rawa yake yi gurin sharar, yana kammala shara harya ɗauko bokitin morping kiran sallar magarib ne ya ratsa dodon kunnen sa.
Ɗan jim ya yi yana shawarar yaje ko ya bari harya kammala?, amman inaáh sai kawai ya ci gaba da morping ɗin.
Sai da ya mayar da Parlourn fess dashi sannan ya yi zaune yana jiran fitowar ta.
Wanka ta feso cikin ƙananan kaya sai ƙamashin turare dake fita daga cikin jikinta, fuskarnan tasha uban make up sai ƙyalli ta ke yi.
Gurin zama ta nema ta zauna tana mai ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya sai faman ƙarewa Parlourn kallo ta ke yi.
Ta gefen ido yake kallon kalar shigar da ta yi, yayinda ita kuwa ta yi kamar bata gansa a gurin ba.
Sunanan zaune kamar kurame aka yi kiran sallar isha'i.
Kallonta ya yi a maraice yana neman yaji ta ce "tashi kaje".
Lura da hakan da ta yi ne ya sanya ta cewa "ɗan bara na gwada naga".
Kallonsa ta yi kana ta ce "tashi kaje masallaci."
Da hanzari ya miƙa, ai kuwa saiji ya yi ta ce "koma ka zauna ba inda zaka".
Komawa ya yi ya zauna kuwa yana me faman sakin murmushin yake.
Sosai ta jinjina wa aikin bokan nata, ta saki murmushin gefen baki tana ayyana irin yadda wannan damar data samu.
★★★★★★
Haka rayuwa ta yi ta tafiya, gaba ɗaya Ƙasim ya fice daga hayyacinsa idan ka ganshi kamar ba Ƙasim ɗin nan bane gayen gaske ba.
Gaba ɗaya baya fita ko ina har gurin aiki ya daina zuwa bauta ka ɗai yake yiwa ZULFA'U, har wankin yanzu shi keyi mata , ita kuwa sai dai ta sanya ƙafa ta kalme ta fice yawon gantalin ta, wani lokacin ta dawo wani lokacin kuwa a can take kwana.
Sosai hankalin Hajiya Umma ya tashi ganin tun ranar daya fice daga gidan ya kimanin mako biyu kenan amma ba shi ba labarinsa, idan an kira sa a waya ma baya ɗagawa idan ancin sa'a ne tana gidan take sa hannu ta danne wayar ta mutu, sai ga shi da tafiya ta yi tafiya gaba ɗaya ma ta ɗauke wayar tasa ta kashe takai can ƙasan bed ta jefar da'ita.
Kallon Hussaina dake zaune tana kuka ta yi kana ta ce "wai anya yaronnan lafiya yake kuwa?".
"Waye Umma?".
"Wancan mijin Hajiya mana, rabon sa da nan tun lokacin da aka gaya masa dawowar ta ya fice da hanzari kamar ya kifa a ƙasa."
"Ko mu shirya muje mu dibo ne?."
"Zaku iya da fitinar matarsa?", ai Umma ba gurinta za mu je ba gidan yayanmu za mu je."
"Tau bara su Uwata, {Maimunatu take nufi cox sunan mahaifiyarta ne hakan} ,su dawo ku shirya ku je dan Allah koda ta yi muku wata tijara karku bi takanta ku yi abin da ya kaiku kawai ku fito."
"Karki damu Umma bara naje na shirya kamin su shigo."
Yau ko da suka tashi da manyan baƙi suka ci karo, Hajiya Turai ce da ƙawarta Ruƙayya wacce suke cewa Ruka yau suka kawo masu ziyara, bakajin komai a ɗakin sai shewarsu a ɗakin.
Cikin ƙasa ƙasa da murya Hajiya Turai ta ce "gaskiya na jinjina wa wannan bokan , ashe haka aiki ya ci ina can gida miƙe da ƙafafuwa?."
"Uhummmm bari Hajja ta, gaba ɗaya yanzu ko ina bana bari ya tafi, duk da sallah fa idan bance yaje ya yi ba wallahi baya yinta, kinga dana buɗe masa idanuwana yake wani fizge fizge?, humm ai yanzu duniya take sabuwa a gurina, ke idan ba da wannan ba Ƙasim ba zai barni na wataya ba, inajin yau saura 2days mu ɗaga zuwa ƙasar Amurika wajen shaƙatawa nida Alhaji na."
Taɓewa suka yi suna ci gaba da buga shewa, ɗan ɗauke fuska ta yi sannan ta ce bara ku ga "Ƙasim!, kira ɗaya ta yi masa ya fito da hanzarinsa jikinsa har rawa ya keyi ya duƙa yana ƙara gaidasu Hajiya Turai kana ya kalleta ya ce "gani", "baka ga na yi baƙi bane da bazaka fito ka ɗaura masa girki da wuri bane halan?."
Jikinsa naci gaba da rawa ya ce "afuwa ranki ya daɗe yanzu nake niyar fitowa."
Ba tare data ce komai ba ta nuna masa hanyar kitchin miƙewa ya yi da sauri ya nufi kitchin ɗin, yayinda Ruka ta bishi da kallon tausayawa, ita dai haka kawai Allah ya sanya mata tausayin bawan Allahn nan ganin yadda Allah ya jarabcesa ta hanyar mace , ko macen shu'uma.
Fitowar sa daga kitchin hannunsa ɗauke da tire saƙe da white rice da miya wacce taji naman kaza zallah sai tururi ta keyi , ya yi dai dai da sallamar da su Hassana su kayi a babban Parlour.
Ko kallon gunda suke beyi ba ya nufi gabansu Hajiya Turai ya janyo Centre table ya ɗaura abincin a sama sannan ya miƙe.
Karaf idanuwansa suka sauka a kan 'yan uwan nasa waɗanda ke kallonsa cike da tausayawa.
Hussaina ce ta ce "Yaya halan ka yi rashin lafiya ne?, kallon ZULFA'U ya yi wacce gaba ɗaya ita da su Turai suka zubo masu idanuwa.
Ganin yadda ya kalleta a marece ya sanya su suma kallon wurinda take zaune, ɗauke kanta ta yi daga gare su ta mayar kansa kana ta buga masa tsawa "kai maza jeka kawowa su Hajiya ruwa da jus mana kazo ka tsare mutane da idanuwa."
Da hanzarinsa ya fice daga Parlourn ya nufi kitchin, fridge ya buɗe ya ɗauko masu ruwa masu sanyi da lemon kwalba ya ɗauro a kan tire ya kawo ya dire masu, ƙara kallon su Hassana ya yi waɗanda ke tsaye har lokacin suna kallon ikon Allah kana ya juya ya kalli ZULFA'U wacce ta mayar da hankalinta kan su Hajiya Turai.
Sun jima a tsaye shima haka yana tsaye kansa a ƙasa ya yin da zuciyarsa yake jin tamkar ta buga ji yake yi kamar ya rufe ta da duka amman inaaah kome yayi niyar aikatawa sai yaji ba zai iya ba.
"To mukam mun wuce , Allah ya saukaƙa ya mayar wa mugu da muguntarsa", muryar Hassana dake wannan maganar ce ta daki dodon kunnen sa.
Ganin har sun samu damar ficewa daga Parlourn ne ya sanya shi duƙar da kansa ƙasa, ji yake yi kamar ya bisu.
Ganin yadda suka dawo a hasale ya sanya Hajiya Umma miƙewa daga wajen da take zaune ta nufi ɗaki.
A tare suka sauke ajiyar zuciya baran ma Maimunatu da jikinta ya sanyaye.
Jikinta ne ya bata ba lafiya ba, ta kalle su tace "lafiya kuwa!".
"Hassana ce ta caɓe maganar da "ina lafiya kuwa Umma?, kinga yadda Yaya ya koma lokaci ɗaya kuwa?".
Nan Hassana ta zayyane mata abinda idanuwansu suka gano.
Shuru ɗakin ya ɗauka kowa yana tunanin abin.
Miƙewa Umma ta yi sannan ta ce "banga ta zama ba ai, bara naje wajen Malam Nasiru ya sanya a yi masa saukar Alƙur'ani ya tanya mu addu'a, don wannan kam sai Allah ya saka mana tsakaninmu da ita."
Haka su Hajiya Turai suka wuni a gidan dukkanin ɗawainiyar su Ƙasim ne ke yin ta , sai bayan isha'i sannan suka fice daga gidan su dukan su har uwar gayyar.
Suna ficewa shima ya fice ya nufi gidan Hajiya Umma, da kukan sa da komai yana bawa Umma haƙuri, janshi ta yi a cikin jikinta tana bashi baki da kuma tofa masa addu'oi a saman kansa, ba jimawa baccin wahala ya kwashe shi.....
A Gobe za mu ci gaba........
ƳAR MUTAN BUBARE.
Maryamah