Halin Da Nijeriya Take Ciki Yafi Muni Kan Lokacin 2015

Halin Da Nijeriya Take Ciki Yafi Muni Kan Lokacin 2015

 

Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magana game da tattalin arzikin Najeriya, yace kasar na cikin halin da ya fi na 2015 muni. 

This Day ta rahoto Khalifan na mabiya darikar Tijjaniya ya yi jawabi a wajen bikin da AAF ta shirya jiya, yace lamarin zai iya kara tabarbarewa a 2023.
Gidauniyar Akinjide Adeosun tayi wani taro a kan shugabanci domin a tuna da Akinjide Adeosun wanda shi ne wanda ya kafa gidauniyar. 
A matsayin babban bako a taron na Legas, Muhammadu Sanusi II yace ya kamata kowa ya damu da tsaro, talauci, hauhawar farashi da darajar Naira. 
“Wannan ce kurum kasa mai arzikin mai da ke kuka a lokacin da farashin mai ya tashi a Duniya a sakamakon yakin Rasha da Ukraine. 
Mun burma rami mai zurfi a 2015, tsakanin shekarar 2015 zuwa yanzu muka cigaba da hakawa kan mu wani ramin da ya fi zurfi.
 
Masanin tattalin arzikin ya nuna masu mulki sun gaza idan ba a iya biyan bashi. Vanguard ta ce Khalifa yana tir da yadda aka rasa shugabanni masu tunani. “Mun yi tunani mun shiga babbar matsala a 2015. Amma 2015 ba komai ba ne idan aka kamanta da abin da zai faru a 2023.