Majalisar Wakilai ta Umarci CBN ya Dakatar da Karbar Harajin Tsaron Yanar Gizo 

Majalisar Wakilai ta Umarci CBN ya Dakatar da Karbar Harajin Tsaron Yanar Gizo 

Majalisar wakilai ta umarci babban bankin kasa da ya dakatar da aiwatar da harajin 0.5 % na tsaro ta yanar gizo kan hada-hadar kudi.
Wannan ya biyo bayan kudirin gaggawa da shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda, ya gabatar a yau Alhamis. 
Sanarwar da babban bankin na CBN ya fitar a ranar Litinin ta ce za a fara aiwatar da harajin ne mako biyu daga ranar da aka sanar da shi, kamar yadda Premium Times ta wallafa.
Tun bayan sanar da harajin da bankin CBN ya yi, ‘yan Najeriya, ciki har da kungiyar dattawan Arewacin kasar nan ke bayyana rashin dacewar hakan saboda matsin da ake ciki. A zamanta na yau, majalisar wakilai ta dubi koken yan Najeriya, inda ta bayyana matakin sanya harajin ta yanar gizo a matsayin kuskure, kamar yadda Intel region ta wallafa. Tun da fari, babban bankin kasa CBN ya umarci bankuna su fara cirar kudin tsaron intanet mako biyu bayan bayar da umarnin, wanda ya ce ya yi daidai da gyaran da aka yi wa dokar tsaro ta internet ta 2024.