Mahaifiyar Sheikh Ahmad Gumi Ta Rasu 

Mahaifiyar Sheikh Ahmad Gumi Ta Rasu 

Mahaifiyar fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan na jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, ta riga mu gidan gaskiya. 

Bayanai sun nuna cewa mahaifiyar Malamin ta rasu ne a wani Asibiti dake birnin tarayya Abuja da yammacin yau Lahadi, 5 ga watan Maris, 2023. 
Shehin Malamin ya tabbtar da rasuwar mahaifiyarsa a shafinsa na dandalin sada zumunta na Facebook. Ya ce ta rasu da misalin ƙarfe 5:30 na yamma. 
"Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, da zuciya mai rauni nake sanar da rasuwar mahaifiyata, yau da misalin karfe 5:30 na yamma. 
Dan Allah ku tama ni roka mata gafara da rahamar Allah." 
"Kalamai na karshe da ta faɗa mun mako uku da suka gabata; In Sha Allah, Allah zai sanya ta da 'ya'yanta da jikokinta wuri ɗaya a cikin gidan Aljannah." 
"Waɗan nan kalmomi suna kwantar mun da hankali, Allah ya tabbatar da rahamarsa a gareta, Amin." 
Wata sanarwa mai biye wa wannan a shafin Malamin na Facebook ta ce za'a yi jana'iza gobe Litinin 6 ga watan Maris, 2023 a ƙofar gidan Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi. 
Sanarwan ta ƙara da bayanin cewa za'a gabatar da Jana'iza da Azahar misalin karfe 1:00 a gidansu da ke Anguwar Sarki, GRA bayan Lugard Hall cikin garin Kaduna.