Sanata Wamakko  Ya Tallafawa Yankuna Huɗu Da Taransfoma Don Fitar Da Su Cikin Duhu

Sanata Wamakko  Ya Tallafawa Yankuna Huɗu Da Taransfoma Don Fitar Da Su Cikin Duhu

Shugaban kwamitin tsaro a majalisar dattijai Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko yau  Laraba ya da kyautar Taransfoma mai ƙarfin wuta 300KVA ga al'ummar mazaɓar Sarkin Zamfara A da B a ƙaramar hukumar Sakkwato ta kudu a jihar Sakkwato.
Sanata ya yi wannan kyautar ne bayan gabatar masa da koken buƙatar ya tallafa domin mutanen yankin sun kashe kuɗi masu yawa a wurin gyaran tsohuwar Taransfomarsu amma ba ta yi ba tsawon lokaci.

Shugaban APC a ƙaramar hukunar Bello Mainasara ya ce sun daɗe cikin baƙar wahalar rashin wutar a yankinsu.
Ya ce lamarin ya shafi mutanen 'Yar Goriba, Unguwar Diresa, Sarkin Zamfara A and B, 'Yar Akija, Sabon Titi da sauransu ne za su amfana da tallafin abin da zai su fita a cikin duhun da suke fama da shi.

Haka ma Sanatan ya ba da irin wannan gudunmuwa ga mutanen Mana Ƙarama da Trade Fair da Sabuwar Bado dukansu ya ba da Taranfomar mai ƙarfin wuta 500KVA da 300KVA da 500KVA.
Sanata Wamakko a tabakin Daraktan mulki Alhaji Almustapha Abubakar Alkali ya ce a koyaushe Sanata shirye yake ya tallafawa mutanen mazaɓarsa kan haka ƙofarsa a buɗe take ga dukkan wasu ƙorafe-ƙorafe. 

Mai taimakawa Sanata a kafafen yaɗa labarai na zamani Bashar Abubakar ya ce ya nemi waɗanda suka amfana su tabbatar an yi amfani da ita yanda yakamata a kuma samar tsaro ga ɓarayin waya da sauran kayan Taranfoma.