EFCC ta gurfanar da Ministan Buhari da 'yarsa a Kotu

EFCC ta gurfanar da Ministan Buhari da 'yarsa a Kotu

An gurfanar da tsohon ministan sufurin jirgin sama Hadi Sirika da 'yarsa Fatima a babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda EFCC ke tuhumarsu da laifuka shida da ke da alaƙa da almundahana na kusan naira biliyan uku.

EFCC wadda ta shigar da karar na zargin ministan ya yi amfani da muƙaminsa ba bisa ka’ida ba ta hanyar ba da kwangilar naira biliyan ɗaya da dubu dari uku domin kafa kamfanin Nigeria Air.

Tsohon ministan da 'yarsa sun gurfana a kotun ne da misalin karfen 9 a yau ranar Alhamis tare da mutum na uku da ake zargi da hannu a lamarin, daga ciki har da Jalal Sule Hamma, wanda surukin Hadi Sirika ne.

Haka zalika a gurfanar da kamfanin Al Duraq Investment a gaban kotun inda aka tuhume shi da hannu a Almundahanar.

Sai dai dukkaninsu sun musanta laifukan da ake tuhumarsu da su.