Bukin Sallah: Mahara Sun kashe mutane 6 sun tafi da wasu a Sakkwato

Bukin Sallah: Mahara Sun kashe mutane 6 sun tafi da wasu a Sakkwato

 

'Yan bindiga dauke da makamai sun shiga kauyen Tudun doki dake cikin karamar hukumar Gwadabawa a jihar Sakkwato sun kashe mutane 6 sun yi garkuwa da wasu mutane masu yawa.

A cewar Ibrahim Adamu maharan sun shiga garin da misalin karfe 11:30 na daren Assabar.
Ya ce 'yan bindigar sun shiga kauyen sun kashe mutum biyar, sai dai ba su san yawan mutanen da aka yi garkuwa da su ba, domin wasu sun gudu domin neman tsira, har sai an ga yawan mutanen da suka dawo ne za a san yawan wadan da ke hannun 'yan bindigar.
Mai magana da yawun 'yan sanda a jihar Sakkwato Ahmad Rufa'i ya ce mutane shida ne 'yan bindigar suka kashe.
"Mutane shida ne muka tabbatar an kashe, kamar yadda asibiti ta tabbatar mana, yawan mutanen da aka yi garkuwa da su ba mu san adadin ba zuwa yanzu, za mu sanar da ku in mun samu bayani mai inganci kan hakan.