Gwamnatin Yobe Zata kashe Sama Da Biliyan 3 Wajen Gina Kasuwar Zamani a Gaidam

Gwamnatin Yobe Zata kashe Sama Da Biliyan 3 Wajen Gina Kasuwar Zamani a Gaidam
 
Daga Muhammad Maitela, Damaturu.
 
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ranar Alhamis ya Kaddamar da dora harsashen ginin sabuwar kasuwar zamani, wadda aka kiyasta za a kashe naira biliyan uku da digo takwas (N3.8bn) wajen kammala ginata, a garin Geidam dake jihar. 
 
Bugu da kari kuma, gwamnatin jihar ta bayar da aikin ginin sabuwar kasuwar ga kamfanin 'Green and Blue', tare da daukar alkawarin kammala aikin cikin watanni 12. Yayin da ya kara da cewa, "Dalilan da suka kawo jinkirin fara aikin kasuwar a baya su ne matsalolin tsaron Boko Haram da suka addabi wannan gari na Gaidam." 
 
Da yake jawabi a wajen Kaddamar da harsashen ginin sabuwar, Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana cewa, makasudin gina kasuwar shi ne domin bunkasa harkokin kasuwanci da na tattalin arziki a yankin, musamman ta la'akari da garin Gaidam a matsayinsa a kan iyaka da Jamhuriyar Nijar, domin ci gaban huldar cinikayya. 
 
Har wala yau, Gwamna Buni ya bude wasu manyan ayyuka a garin, wadanda suka kunshi bude cibiyoyin kiwon lafiya guda biyu, tare da bai wa Ma'aikatar ayyuka ta jihar da hukumar kula da gyara hanyoyi ta jihar umurnin gyara hanyar Gaidam zuwa Maini-Sorowa, hanyar Gaidam zuwa Garin-Gada zuwa Bukarti kana da Kaddamar da bude Makarantar Mega, hanyar mai tsawon kilomita biyu duk a cikin garin Gaidam. 
 
A hannu guda kuma, Gwamna Buni ya bai wa Shugaban karamar hukumar, Sarakunan gargajiya umurnin hada kai da dan kwangilar wajen ganin an kammala aikin sabuwar kasuwar bisa ka'ida.
 
Haka zalika kuma, Gwamna Buni tare da jiga-jigan jam'iyyar APC a jihar, sun halarci gangamin yakin neman zaben shiyya ta daya (Zone A) wanda ya gudana a babban filin wasanni dake garin Gaidam wanda ya samu halartar manyan baki tare da dubban magoya bayan jam'iyyar APC.