Jihohin da PDP ke mulki ne kawai za ka ga ana ƙaddamar da aiyukkan cigaba------Tambuwal
Jihohin da PDP ke mulki ne kawai za ka ga ana ƙaddamar da aiyukkan cigaba------Tambuwal
Shugaban ƙungiyar Gwamnonin PDP kuma Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya ce jihohin da PDP ke mulki ne kawai za ka ga ana ƙaddamar da aiyukkan cigaba da aka yi don al'umma, gwamnoni su cigaba da hakan.
Hakan ke nuna jihohin da ba PDP ce ke mulki ba gwamnonin nasu ba sa komai na cigaban jama'a tun da ba a ƙaddamar da aiyukka a wuraren.
Gwamna Tambuwal ya faɗi haka a wurin taron majalisar zartarwar jam'iyar PDP(NEC) wanda aka gudanar a hidikwatar jam'iyar a Abuja yau Assabar ya ce jihohin PDP ne kawai ake ƙaddamar da aiki a Nijeriya.
Ya ce za su ci gaba da goyawa jam'iyarsu baya ta samu nasara domin 'yan Nijeriya na jiran PDP domin ta ceto su da halin da suke ciki.
Tambuwal ya ƙara da cewar "Ba za mu iya nasara ba matuƙar mun rarrabu, mu haɗa kai don samun nasara,da ikon Allah PDP za ta karɓi Nijeriya a 2023."a cewar Tambuwal.
managarciya