Daga Aminu Abdullahi Gusau.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta kwato shanu 69 daga hannun ‘yan bindiga a lokacin da jami’an ‘yan sandan suka dakile harin da aka kai kauyen Tudun Masu dake karkashin gundumar Karakkai a karamar hukumar mulkin Bungudu dake jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ayuba N. Elkana, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai, yau laraba.
Inda ya ce, “A ranar 19 ga Disamba, 2021 da misalin karfe 1400 na safe, jami’an tsaro na ‘yan sanda karkashin jagorancin DPO Bungudu sun amsa kiran gaggawa a Tudun Masu inda ‘yan bindiga da dama suka kai farmaki kauyen suka yi awon gaba da shanu sittin da tara (69),”
A cewarsa, daga cikin shanu 69 da aka kwato, 60 daga cikin su amba da su ga ainihin masu su bayan an tantance sannan aka mika musu, sauran tara (9) kuma an mika su ga kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa domin karbar dabbobin da aka sace kuma aka gano su domin ci gaba da daukar mataki.
Ya yi nuni da cewa, jami’an rundunar sun kashe ‘yan bindiga da dama a Bayan Ruwa a karamar hukumar mulkin Maradun, sun kuma kwato bindigu AK-47 (8) Bindigogi guda daya kirar (GPMG), roka daya, da dai sauran su.
“A ranar 15 ga Disamba, 2021, jami’an ‘yan sanda namu da ke aikin a dajin Maradun, sun kai farmaki kan maboyar ‘yan bindiga da ke kusa da Bayan Ruwa,” in ji shi.
Kwamishinan ya yi kira ga al’ummar jihar da su rika kai rahoton duk wani bako wanda basu sani ba, ko kuma wani motsi da mutanen banzan ke yi a yankinsu ga ‘yan sanda domin su dauki martani cikin gaggawa.





