Kotu ta ci tarar gwamnatin Kano N10m bisa barazanar kama Sarki Aminu Bayero 

Kotu ta ci tarar gwamnatin Kano N10m bisa barazanar kama Sarki Aminu Bayero 

Kotun tarayya a jihar Kano ta umarci gwamnatin jihar da ta biya tuɓaɓɓen Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero bisa tauye ƴancin sa na ɗan ƙasa.

Tun a ranar 27 ga watan Mayu ne Bayero, ta hannun lauyan sa, ML Yusufari ya shigar da korafi a gaban kotun da ta hana gwamnatin Kano kama shi ko yi masa barazana ko tauye masa hakkinsa na ɗan ƙasa.

Da ya ke yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari'a Simon Amobeda, ya ce umarnin da gwqmman Kano Abba Kabir Yusuf ya bayar na kama Bayero ba tare da ya aikata wani lefi ba ya zama barazana ga ƴancin sa na ɗan kasa.

Alkalin yace sashi na 35(1) ne na kundin tsarin mulki na 1999 ya bada damar ƴancin ɗan kasa.

Tun a 23 ga Mayu ne dai gwamna Abba ya saka hannu a dokar da ta rushe dukkan masarautu 5 na jihar, inda ya dawo da Sarki Muhammadu Sanusi ll.