Kotu ta bada belin Alhassan Ado Doguwa

Kotu ta bada belin Alhassan Ado Doguwa

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta bayar da belin shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, wanda da ke fuskantar tuhumar kisan kai.

Mai shari’a Yunusa Mohammed, wanda Hukumar Kula da Fannin Shari'a, NJC ta taba tuhumarsa da laifin cin hanci da rashawa neya bayar da belin dan majalisar a yau Litinin.

An fara gurfanar da Doguwa ne a ranar 1 ga watan Maris a gaban wata kotun majistare da ke Kano bisa laifin kisan kai, hada baki, barna, mallakar makami ba bisa ka’ida ba da kuma tada hankali.

Sauran wadanda ake tuhumar sun hada da Nazifi Asnanic, Nafiu Musa, Hamisu Amadu da Abdulhadi Alaramma.

An tuhumi Alhassan Doguwa ne da laifin kona wani gini da ya yi sanadiyar kona Alasan Mohammed da Aminu Malam Amadu har lahira, yayin da Bashir Yani, Labaran Sule da Amadu suka samu raunuka sakamakon gobarar.

Laifukan sun sabawa sashe na 97, 114, 247, 336 da 221 na kundin Shari'a na Penal Code.