Gwamnatin Kano ta yi kira ga Tinubu da ya gaggauta ɗauke Sarki Aminu daga gidan Nassarawa 

Gwamnatin Kano ta yi kira ga Tinubu da ya gaggauta ɗauke Sarki Aminu daga gidan Nassarawa 

Gwamnatin jihar kano ta yi kira da babbar murya ga shugaban kasa, Bola Tinubu da ya gaggauta dauke Sarkin Kano na sha biyar, Aminu Ado Bayero daga jihar.

Gwamnatin ta ce hakan shi ne masalaha, la'akari da yadda wasu ke anfani da wannan damar wajen neman tayar da husuma a fadin jihar.

Freedom Radio ta rawaito cewa Mataimakin Gwamnan jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya yi kiran, inda ya nuna cewa zaman Bayero a gidan Nassarawa anyi shi ne da wata manufa domin hana jihar ta zauna lafıya da kuma kin yi wa al'ummar jihar abin da ya dace.

Haka zalika Gwarzo ya ce zanga-zanga da al'umma suka fito a wannan satin, al'umma suna da hakkin fitowa domin nuna goyon bayan su kan abin da suke so, da suke bukatar a cire sarkin kano na sha biyar daga gidan Nasarawa amma aka turo jami'an tsaro suka hana su tare da kama wasu daga ciki.

Gwarzo ya kuma ce su na kira ga shugaban kasa da ya gaggauta dauke Bayero ya maida shi garin su domin barin al'umma su zauna lafıya.

Gwarzo ya kara da cewa doka ce ta cire Bayero ta kuma dawo da Khalifa Muhammadu Sanusi ll, inda ya ce "don haka a bar doka ta yi aikin ta."