Sojoji sun kashe wani babban ɗan ta'adda a Borno
Sojojin Najeriya sun kashe wani ƙasurgumin kwamandan ’yan ta’adda mai Amir Abu Fatima da aka sanya ladar Naira miliyan 100 ga duk wanda ya kama shi ko ya tona asirin inda yake, aka kama shi.
Sojoji sun kama Abu Fatima ne da ransa bayan musayar wuta a wani samame na musamman a safiyar Juma’a a yankin Kukawa da ke yankin Tafkin Chadi a Arewacin Jihar Borno.
Daga bisani ya mutu a hannun sojoji a sakamakon zubar da jini fiye da ƙima daga raunukan harbi da ya samu a yayin musayar wuta.
Abu Fatima yana daga cikin jerin ’yan ta’addan da jami’an tsaro ke nema ruwa a jallo saboda hannu a hare-haren ta’addanci a yankin Tafkin Chadi.
managarciya