Matashi ya kashe kansa bisa zargin satar wa mai gidansa N100,000
Wani matashi dan shekara 17 mai suna Ojibe Chibueze, ya mutu sakamakon kashe kansa bayan da aka zarge shi da satar kudin ubangidansa.
Kakakin rundunar ƴansanda a jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa hakan a jiya Laraba.
Hundeyin ya ce wata Cynthia, wacce aka ce yayar yaron ce ta kai rahoton ga ofishin ƴansanda na Elemoro a jiya Laraba da misalin karfe 7.50 na safe.
Ya ce matar ta ruwaito cewa dan uwanta, Ojibe Chibueze, ya dawo daga aiki ranar Talata da misalin karfe 8:00 na dare.
Matar ta ce dan uwanta ya dauki wasu kudi ya fita, inda ta jaddada cewa daga baya ubangidansa ya kira ya sanar da ita cewa ɗan uwanta ya ɗaukar masa Naira 100,000 a shagonsa.
Matar ta ci gaba da cewa dan uwanta bai dawo gida ba har sai da makwabcin ta ya buga waya, inda ya sanar da ita ganin gawar dan uwan a kwance a Abijo Bus Stop, Ajah, Ibeju-Lekki, Legas.
"An ga kwalbar fiya-fiya a matsayin shaida. An dauke gawar kuma an ajiye ta a dakin ajiye gawawwaki na babban asibitin Epe domin adana ta,” inji Hundeyin.
Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
managarciya