Naira 52 ne farashin litar man fetur a Libya -- Rahoto

Naira 52 ne farashin litar man fetur a Libya -- Rahoto

Kasar Libya na ci gaba da siyar da man fetur mafi araha a Afrika inda ake siyar da duk lita 1 kan Naira 52 a canjin kudin Nijeriya.

Hakan na kunshe ne a rahotan farashin mai na kasashen duniya.

Farashin man a Egypt da Algeria da Angola yana kan farashin dala 0.279 da dala 0.342 da kuma dala 0.351 a duk lita.

Wadannan su ne kasashen Afrika 4 dake siyar da mai mafi Araha da suka fi Nijeriya.

Rahotan baya bayan nan ya nuna cewa, mafi karancin farashin litar mai a Nijeriya shi ne N1, 000 inda farashin yake kai N1, 600 a kasuwar bayan fage.

Agefe guda kuma, kasar Afrika ta tsakiya ita ce inda ake siyar da litar man mafi tsada a Afrika kan Dala 1.83.

Duk da kasancewar ta kasar da ta fi fitar da mai a Afrika, Nijeriya na shan suka kan siyar da man da tsada.