Kotu ta dakatar da zaɓen ƙananan hukumomin APC  tare da Mai Mala Buni

Kotu ta dakatar da zaɓen ƙananan hukumomin APC  tare da Mai Mala Buni
Kotu ta dakatar da zaɓen ƙananan hukumomin APC  tare da Mai Mala Buni

 Babbar Kotun da ke zama a Asaba, jihar Delta, a jiya laraba, ta dagakatar da Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe da sauran mambobin kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC daga yin aiki kuma su daina  nuna kansu a matsayin shugabannin jam'iyyar har zuwa lokacin da za a yanke hukunci a gaban kotun.

Kotun, wacce Mai Shari’a Onome Marshal Umukoro ke jagoranta, ta kuma dakatar da babban taron APC na kananan hukumomi da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar, 4 ga Satumba, 2021 a Jihar ta Delta.
Hakan ya biyo bayan karar da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC a jihar Delta, Olorogun Elvis Ayomanor, ya shigar a kotun biyo bayan rikici da ya barke ranar 10 ga watan Yuli, 2021, sakamakon zaben gundumomi da aka gudanar a fadin jihar.

Yanzu abin jira a gani matsayar da jam'iyar za ta fitar kan wannan hukuncin domin har yanzu ba ta ce komai kan batun ba.