Duk Da Dokar Taɓaci Kan Ilimi A Sokoto, Makarantar Furamare Ta Ruggar Giwa Na Cikin Mawuyacin Hali
Daga Aminu Alhussaini Amanawa, Sokoto.
Makarantar Primaryn Ruggar Giwa dai na a kauyen Tuntube ne dake yamma ga garin Shuni na karamar hukumar mulkin Dange-shuni dake jihar Sokoto, tafiyar a kalla mintuna 15 zuwa 20 daga kauyen zuwa kwaryar birnin Sokoto.
Makarantar wacce aka kafa sama da shekaru 40 da suka gabata, na cigaba da kasancewa cikin halin ka’ka’ni kayi, na lalacewar azuzuwa, da ofishin shugaban makaranta, dama na malamai, uwa uba rashin kayan rubutu dana karatu da makarantar Primaryn ke fama dashi.
A cewar daya daga mazauni kauyen Malam Muhammad Naira Tuntube, yanayin da makarantar ke ciki na jefa tunanin su cikin halin ni’yasu.
"Mukan kasance cikin bakin ciki a duk lokacin da muka dubi tsan-tsar halin da wannnan makarantr ke ciki da yaran mu ke karatu, wacce aka kafa tun a shekarar 1970, duk da yake cewa bamu da matsalar malamai a wannan makarantar, amma halin da makarantar ke ciki abun damuwa ne matuka".
Shima da yake magantawa shugaban kungiyar iyayen yara da malamai na makarantar da ya nemi a sakaya sunan sa, ya bayyana cewa duk da kokarin da kwamitin da yake jagoranta keyi, lamarin da makarantar ke ciki na son gagarar kundila.
" A matsayin mu na kwamitin iyayen yara da dalibai na wannan makarantar, muna kokari na ganin iyaye sun tura yara makaranta, duk kuwa da halin da makarantar ke ciki, amma duk da haka anamu bangaren muna kokari wajen samar da Runfuna duk dai domin tabbatar da cewa yaran mu sun samu ingataccen ilimi da zasu zamo masu amfani ga al’umma nan gaba kadan.".
Duk da lalacewar da makarantar tayi a yanzu makarantar kauyen nada sama da dalibai 100 da suke karbar darussa a kasa da sa’oi 3 zuwa 4 a cewar daya dag acikin dalibban makarantar.
" Muna karantar da yara ne na sa’oi 3 zuwa hudu a rana, watau daga karfe 8n zuwa 12 na rana, saboda a wannan lokacin rana zata soma zafi, abinda yake da matukar wahala ga yaran su iya samun damar daukar darussa kan abinda ake koya masu, dan haka ne nake kira ga masu ruwa da tsaki dan Allah su duba halin da wannan makarantar ke ciki su kawo mana dauki.”.
A cewar da dama daga wadanda wakilin namu ya zanta dasu, sun bayyana rashin jin dadin su, kan halin da makarantar tasu ke ciki, duk kuwa da cewa suna bada tasu gudunmawa wajen jefa kuri’u da kan kai shuwagabanni kan madafun iko.
Koda yake wannan makarantar na cikin wani hali, amma hakan bai hanawa yaran dake karatu a ciki ba, fatan zamowa wani abu nan gaba a rayuwa.
"Sunana Hafsat daliba a wannan makarantar Ta Ruggar Giwa inada burin son zama abubuwa da dama a rayuwa nan gaba, amma halin da makarantar mu ke ciki na sanya ni damuwa, kan ko burin nawa zai iya cika”.
Da halin da makarantar ke ciki dai a yanzu hakimin kauyen yayi kira da babbar murya na akawo masu dauki domin magance masu abubuwan da suke bukata, da zai bawa malamai damar gudanar da ayukkan su, yanda yakamata.
Sai dai lokacin da aka tuntubesa daraktan wayar da kan jama’a na hukumar bayar da ilimi bai daya ta jihar Sokoto Dr Kabiru Aliyu, ya bayyana cewa sam basa sane da halin da makarantar ke ciki, amma da samun wannan labarin zasuyi duk mai yuwa wajen magance wannan matsalar.
“Kamar yanda kowa ya sani gwamna Aminu Waziri Tambuwal nayi hubbasa a wannan bangaren, musamman ilimi matakin farko dama na gaba da sakandiri, kuma da yardar Allah zamuyi wani abu akai, kari da hakan na zuwa ne sa’ilin da sabon shugaban hukumar Altine Shehu Kajiji ya dukufa wajen kai ziyara a makarantun nan Primary dake fadin jihar Sokoto, domin duba halin da makarantun ke ciki, da lalubo hanyoyin tallafa masu domin shawo kan matsalolin inji shi”.
"Kuma ina bawa al’ummar kauyen Ruggar Giwa ta karamar hukumar mulkin Dange shuni cewa, bada bata lokaci ba zamuyi wani hubbasa akai”.
Idan dai za’a iya tunawa a shekarar 2015 gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya ayyana dokar daukin gaggawa a bangaren ilimin jihar Sokoto.
managarciya