Cire Tallafin Fetur: Tunanin Tinubu Ya Sha Bamban da Mutanen Nijeriya

Cire Tallafin Fetur: Tunanin Tinubu Ya Sha Bamban da Mutanen Nijeriya
 

Shugaba Bola Tinubu ya dage kan cewa matakin da gwamnatinsa ta dauka na cire tallafin man fetur ya zama wajibi domin hana kasar fadawa cikin fatara.

Tinubu ya sanar da daina biyan tallafin man fetur ne a ranar da aka rantsar da shi tare da furta kalmar “biyan tallafi ya kare”.
Sai dai matakin ya sa farashin kayayyaki ya tashi sama, lamarin da ya kara wahalhalu a kasar bayan da  rufe iyakokin kasar ya kara ta'azzara lamurra. 
Halin kunci da kasar ta tsinci kanta ya sanya wasu daga cikin masu sukar gwamnatinsa suka yi Allah wadai da janye tallafin, suna masu cewa babu hangen nesa a daukar matakin. 
Amma Tinubu ya bayar da hujjar cire tallafin man fetur, yana mai cewa ana bukatar a sake farfado da tattalin arzikin kasar ne farko a kan komai, rahoton Channels TV. 
 
Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a matsayin daya daga cikin mahalarta taron tattalin arzikin duniya da ke gudana a birnin Riyadh na kasar Saudiyya a safiyar yau. 
"Ga Najeriya, mun yi imanin cewa haɗin gwiwar tattalin arziki da haɗa kai ya zama dole domin samar da daidaito a lamuran sauran kasashen duniya. 
"Game da batun cire tallafin fetur, ko shakka babu ya zama wajibi domin kare kasata daga fadawa talauci, da kuma sake saita tattalin arziki da hanyar ci gaban kasar."
Tunanin Shugaban kasa Bola Tinubu ya sha bamban da mutanen Nijeriya in da mafiyawan mutane ke ganin tallafin ne zai taimaki tattalin arzikin kasa domin samun sauki a wurin talaka shi ne tattalin arziki ba tarin dukiya ba.