'Yan sanda sun kama wasu gungun barayin mota a Sokoto

'Yan sanda sun kama wasu gungun barayin mota a Sokoto

 
 
Rundunar 'yan sandan jihar Sakkwato sun yi nasarar kama wasu gungun barayin mota su biyu Austin Anthony mai shekara 44 da Mansur Abubakar mai shekara 32, bayan da suka yi aika-aikar a jihar Sakkwato
Jami'in hulda da jama'a na rundunar a jiha ASP Ahamad Rufa'i ne a bayanin da ya rabawa manema labarai ya ce a satin da ya gabata ne wasu mutum biyu Adamu Muhammad da Kabiru Shehu dake unguwar Badon Barade suka kawo koken a sace wa kowanensu  mota Korolla LE da Pontiac Vibe.
"Bayan da muka samu labarin sai rundunar mu ta dauki mataki in da ta sanar jami'anmu dake shingen hanyar Birnin Kebbi a garin Bodinga.
"A binciken da muke yi wadanda ake zargi sun amsa laifinsu kan haka an gano wasu karin motoci biyu a hannunsu, an kuma kama wani mutum daya."
Ya ce Anthony  'yan sanda sun taba kama shi da zargin ya satar motoci uku sai yanzu kuma an sake kama shi da irin laifin. Da zaran an kammala bincike za a kai su kotu.
"Runduna 'yan sanda karkashin kwamishina Ahmed Musa ta yi kira ga al'umma su zama a fadake su rika bayar da bayanin duk wani abu da ba su gamsu da shi ba ga hukumar 'yan sanda mafi kusa da su, ga nambar wayar kar-ta-kwana da hukumar ke amfani da ita: 08032345167.," a cewarsa