SERAP ta buƙaci Tinubu da muƙarabansa su bayyanawa duniya kadarorin su
Kungiyar tattabatar da gaskiya wajen gudanar da mulki ta (SERAP) ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya nemi Hukumar Kula da da'ar Ma’aikata (CCB) ya fitar mata da bayanan kadarorinsa.
Kungiyar ta kuma yi kira ga Shugaban kasa da ya baiwa Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima; ministoci; shugabannin Majalisar Tarayya; gwamnonin jihohi; da shugabannin kananan hukumomi 774 na Najeriya umarnin su kuma nemi CCB ta bayyana kadarorinsu.
Daily Trust ta rawaito cewa a wata wasika mai kwanan watan 28 ga Disamba, 2024, wadda mataimakin darakta a SERAP Kolawole Oluwadare, ya sanya wa hannu, SERAP ta ce:
“Muna maraba da matsayar da aka ruwaito cewa za ku yi la’akari da tambayar CCB ta fitar da kadarorinku a matsayin cigaban da ya dace, da kuma wata alama ta shirin, da kuma jajircewarku wajen nuna jagoranci a wannan muhimmiyar al’amari da ya shafi jama’a.”
managarciya