Gidauniyar Bafarawa ta ware miliyan 250 don sayawa 'yan gudun hijira da mabuƙata abinci a Sokoto
Gidauniyar Attahiru Bafarawa, ta kebe kudi Naira Miliyan Dari Biyu da Hamsin (#250,000:00) dan Sayen Abinci da raba ga Yan Gudun Hijira da Mabukata a cikin kananin hukumomin jihar Sokoto 23.
inda aka soma da Rabawa wasu 'yan gudun hijirar kananin Hukumomin Rabah,Isa da Sabon Birni Buhuwan Abinci da kudi.
Kwamitin Gidauniyar Attahiru Bafarawa ta Soma Aiki ta Rabawa Yan gudun Hijirar Gandi ....Buhuhuwan Abinchi Guda Dari Biyu (200) da kudi Naira Miliyan Biyu.....#2,000,000 Tun daga Farko Shugaban babban kwamitin Malam Muhammad Muhammad Lawal Maidoki Sadaukin Sakkwato Ya bayyana cewa an soma aikin tare da kaddamar da rabon abincin ga Sansanin Yan gudun hijra na Gandi da ke karamar Hukumar mulkin Rabah, shugaban ya bayyana cewa Maigirma tsohon Gwamnan jihar Sokoto ne Dr Attahiru Bafarawa ya kafa kwamitin domin zakulo bayin Allah mabukata da zaa tallafawa a fannonin Tallafin Abinci,Lafiya,Samar da Ruwan sha,Ilimi, Sana'a da sauran su.. cikin wani Shiri da akayiwa lakabi da "Maida Alheri da Aikin Alhairi"
Shugaban ya bayyana cewa A ranar Jimua 04/10/2024...01-Rabius Sani 1446 an kaddamar da shirin ne da soma baiwa yan gudun Hijira na kananin hukumomin Rabah,Isa da Sabon Birni ... ya bayyana cewa sauran fannonin tallafin suma zaa cigaba da gabatar da su bada Jimawaba..
yayi Kira ga Wadanda suka amfana da suyi Addua ga Wanda ya badaba Tallafin, da duk mai hannu a cikin aikin Alkharin.
Shugaban yayi godiya ga Gwamnatin jihar Sokoto, Fadar Mai martaba,yan kwamitin da duk mai hannu a cikin...wannan aikin jin Kan Alummah ya roki Jamaa da suyi masu Addua dan safke wannan nauyin, a Gandi, Magidanta Yan Gudun Hijira kusan Dubu da Dari biyar ne za su amfana.
Wakilin Yarin Gandi Alh. Yahaya kabir, Shugaban kula da sansanin Malam Ibrahim Ahmad Wakilin yan Gudun hijira kuma hakimin Tabanni,Mal Lawal dukkan su sunyi godiya da addu'ar Allah ya saka da Alkhairi.
A Garin Rabah Malam Kabiru shehu Binji da Nura Abdullah Attahiji suka wakilci Shugaban tare da Alh Ahmad gyrabshi,Malam Sidi Gandi da Mukhtar A Haliru.
Inda wakilin ya bayyana cewa an bada buhuwa guda 50 ne da kudi Naira dubu Dari biyar (#500,000:00) A Rabah, taron ya samu halartar Wakilin Ubanksa da sauran mambobin kwamitin.
Taron anyi shine a wani Sansanin yangudun hijirar da ke cikin garin Assabar 05/10/2024.
A rana ta Ukku Lahadi 6/10/2024, anje Garuwan Isa da Sabon Birni, inda tawagar ta kun shi, Manbobin Babban kwamitin da suka hada Alh. Nasiru Chiroman Bafarawa, Alh. Ahmad Yahya Dada, Alh. Ahmad Gyarafshi tare da Malam Nura Attajiri da Kabiru Shehu Binji, Mukhtar A Haliru Suka shaihid kaddamar da taron a garuruwan Sabon birni da Isa, a sansanin yan gudun hijirar da ke cikin garin Sabon birni, inda Shugaban kwamitin da ya kula da aikin Prof. Yakubu Gobir ya bayyana yadda suka zakulo yan gudun hijirar a Sansani, 7 da Iyalai 1,750 suka amfana, Shugaban karamar Hukumar Mulkin Sabon birni da wakilin yan gudun hijirar duk sun bayyana jin dadin su da Addua ga Tsohon Gwamna da sauran masu hannu a ciki.
A Garin Isa, Alh. Basharu isa Guyawa ( Shugaban Rundumar Adalci) ne ya bayyana yadda suka yi na su tsarin da tantance yan gudun hijirar da suka zakulo cikin Sansanin yan gudun hijirar 5 da zakulo mutun 1,500 suka amfana, uban kasar isa, Sarkin Gobir na isa Alh. Nasiru Ahmad , wakilin wadan da suka amfana sunyi godiya da fatar Alheri.
jadawalin Rabon kayan ya nuna
1.A Karamar Hukumar Rabah sun Samu Buhuwan 250 inda Iyalai 1,763 suka amfana.... a cikin sansanin Yan Gudun Hijira 20 da ke Gandi da Rabah da kudi Naira Miliyan Biyu da Rabi (#2,500,000:00)
2. A karamar Hukumar Mulkin Isa, Buhuhuwa 300 inda Iyalai 1,500 suka amfana da Kudi Naira Miliyan Ukku (#3,000,000:00) a Sansanin Yangudun Hijira Guda Biyar da ke nan Garin Isa, yayin da
3. Karamar Hukumar Mulkin Sabon Birni suka amfana da Buhuhuwan 350 in da iyalai 1,700 suka amfana....a Sansanin bakwai ...da ke Sabon Birni. da Kudi Naira Miliyan Ukku da Rabi (#3,500,000:00).
Shugaban babban kwamitin Maigirma Sadaukin Sakkwato, ya bayyana cewa a yanzu an fara ne da wadannan yan gudun hijirar duba da ganin suna cikin tsananin Bukata, da suke ciki yayin da sauran kananin hukumomin 20 za ayi na su bada Jima ba.
Sannan za'a cigaba da sauran Ayukkan jinkan
managarciya