Sabbin bayanai kan 'yan bindiga da suka sace mutum 30 lokacin sallar asuba a Zamfara
Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewacin ƙasar na cewa aƙalla mutum 30 ne wasu ‘yan bindiga suka sace a ranar Alhamis a wani masallaci da ke ƙaramar hukumar Tsafe a lokacin da suke sallar asuba.
Haka kuma wasu maharan sun mamaye garuruwa da dama a ƙaramar hukumar Dansadau inda suka kashe mutane da dama suka kuma yi garkuwa da ƙarin wasu ciki har da mata.
Garuruwan Dankurmi da Farin Ruwa da Tungar Kawo da Dan Ma’aji da sauran su da ke ƙananan hukumomin Dansadau da Maru da kuma Tsafe dukansu a jihar ta Zamfara, kan fuskanci sabbin hare-haren 'yan bindigar ne kusan ko da yaushe a kwanan nan.
Mazauna garuruwan sun shaida wa BBC cewa ko a safiyar yau Alhamis, wasu mahara sun sace kimanin mutum 30 lokacin da suke tsaka da sallar asuba a garin Tsafe.
Baya ga satar jama’a da maharan suka yi domin neman kuɗin fansa, sun kuma ce suna sakin dabbobi a cikin gonaki su cinye musu amfanin gonar da suke nomawa, a lokaci guda kuma su harbi duk wanda ya yi magana, kamar yadda wani manomin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa BBC.
"Saboda ba mu samu mun yi noma da damina ba, to noman bakin fadama muke yi. Da damina sun addabemu sun kashe mana mutane, sun sace mutane, hakan ya hana mutane da dama su yi noma.
"Duk abin da muka noma sun kwashe. A baya a ƙauyukan da ba sa samun kuɗin fansa kashe mutane suke yi kawai su wuce," in ji manomin.
Ko a garin Farin ruwa da ke karamar hukumar Maru kuwa, kusan haka abin ya ke in ji wani mazaunin garin.
"Ko yanzu maganar da muke yi da ku BBC wallahi hari suke kawo mana. Babura za su kai 50 ko 45.
"Idan har ka yi sa a ba su kashe ka ba, to sai su sace ka su yi daji da kai. Babu jami'an tsaro a nan kwata-kwata."
managarciya