Za mu yi bincike kan harin bam ɗin da ya kashe ƴan-ba-ruwa-na bisa kuskure a Sakkwato - Minista
Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya ce gwamnatin taraiya za ta yi cikakken bincike kan harin bam ta sama da ya yi sanadiyar rasuwar mutane 10 a ƙauyukan Gidan Bisa da Runtuwa a ƙaramar hukumar Silame da ke Sakkwato.
Abubakar Bawa, Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan Sakkwato ne ya baiyana haka a wata sanarwa a yau Asabar a Abuja.
A cewar Bawa, Matawalle ne ya bada wannan tabbacin lokacin da ya kai wa gwamnan jihar, Ahmed Aliyu ziyarar jaje a Sakkwato.
Bawa ya ruwaito ta bakin Matawalle cewa gwamnati za ta tabbatar an yi wa iyalan wadanda su ka rasu adalci, inda ya ce ya bada tabbacin kare rayuka da duniyoyin ƴan Nijeriya s duk inda su ke a fadin ƙasar.
managarciya