Majalisa Ta Dauki Mataki Kan Kudirin Sabon Mafi Karancin Albashi da Tinubu Ya Mika 

Majalisa Ta Dauki Mataki Kan Kudirin Sabon Mafi Karancin Albashi da Tinubu Ya Mika 

 

Majalisar dattawan Najeriya ta yi gaggawar amincewa da ƙudirin dokar mafi ƙarancin albashi na ƙasa na shekarar 2019 (wanda aka yiwa kwaskwarima). Majalisar ta amince da ƙudirin dokar ne a yayin zamanta na ranar Talata, 23 ga watan Yulin 2024.

Tashar Channels tv ta ce ƙudirin dokar ya samu karatu na ɗaya da na biyu da na uku tare da amincewa da shi ƴan mintoci kaɗan bayan an gabatar da shi a gaban majalisar. 
Majalisar ta amince da kuɗirin ne bayan ya tsallake karatu na uku inda duka sanatocin suka kaɗa ƙuri'ar amincewa da shi, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.