Tinubu da Buhari ba sa fadawa ƴan Najeriya gaskiya game da halin da kasa ke ciki, in ji Sule Lamido 

Tinubu da Buhari ba sa fadawa ƴan Najeriya gaskiya game da halin da kasa ke ciki, in ji Sule Lamido 

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya zargi Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da kin fadawa ƴan Najeriya gaskiyar halin da kasa da kuma mulkinsa ke ciki.

Lamido ya kuma zargi tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da rashin bayyana gaskiya ga ƴan Najeriya a lokacin mulkinsa.

Ya yi wadannan zarge-zargen ne  a shirin BBC Hausa mai suna ‘Gane Mini Hanya’, wanda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Lamido ya ce gwamnatocin biyu sun fi mayar da hankali kan yada labaran da ba na gaskiya ba, maimakon su bayyana wa 'yan kasa ainihin halin da Najeriya ke ciki, sabanin lokacin da PDP ke mulki.

Haka kuma, Lamido ya soki bukatar karbar bashin da Shugaba Tinubu ke yi, yana mai cewa “abinda gwamnati ke fadawa 'yan Najeriya ya bambanta da abinda ta ke aiwatarwa.”