Miyati Allah Sun Ja Kunnen Gwamnatin Sokoto Kan Martabar Sarkin Musulmi

Miyati Allah Sun Ja Kunnen Gwamnatin Sokoto Kan Martabar Sarkin Musulmi

Ƙungiyar fulani ta Miyati Allah ta ƙasa sun nuna rashin amincewarsu kan zargin da ake yi cewa gwamnatin Sokoto na yunkurin cin zarafin Sarkin Musulmi in da suka bayyana cewa kare martabar masarautar yakamata su yi a Nijeriya.
Shugaban kungiyar a Nijeriya Alhaji Baba Usman Ngelzama ne ya sanar da hakan a bayanin da ya fitar a Abuja.
Ya ce masarautar da ta shafe sama da shekaru 200 bai kamata 'yan siyasa su rika wasa da ita ba, yakamata su mayar da hankali wajen samar da gwamnati ta gari.
Ya ce kare martabar masarautar Sarkin Musulmi abu ne da ya rataya kan duk wani mai tunani mai kyau a Nijeriya.
Ya yi kira ga gwamnati da Majalisar dokoki su yi abin da zai kare martabar masarauta kar su yi abin da wargaza lamarinta.