Sanatocin Arewa Sun Yi Tir Da Harin Jirgin Ƙasa:Dole Ne Mu Kawo Ƙarshen Wannan Matsalar 

Sanatocin Arewa Sun Yi Tir Da Harin Jirgin Ƙasa:Dole Ne Mu Kawo Ƙarshen Wannan Matsalar 

 

Ƙungiyar sanatocin Arewa sun yi tir da farmakin da aka kaiwa jirgin ƙasa wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna.

Harin wanda ya faru kan hanyar Kateri-Rijana a jihar Kaduna a daren Litinin.

Jirgin ya doshi Rigasa in da zai yi tsayawar ƙarshe sai ga lamarin ya auku in da 'yan bindiga suka buɗe  wuta anan take suka kashe wasu fasinjoji wasu kuma suka samu munanan rauni.

A bayanin  da Aliyu Magatakarda Wamakko Sanata mai wakitar yankin  Sakkwato ta Arewa kuma shugaban dandalin Sanatocin Arewa  ya fitar ya ce 'yan kasa nagari sun rasa rayukkansu a hannun shirmammun 'yan ta'adda.
Wamakko ya ce dole ne a dauki matakin dakatar da kashe mutanen kasa.
Ya ce daukar matakin ba na jami'an tsaro kadai ba ne har da mutanen kasa akwai bukatar hada hannu domin magance matsalar
"Muna yiwa shugaban kasa da gwamnatin Kaduna da iyalai da 'yan uwan wadanda suka rasa rayukkansu ta'aziyar rasa mutanen da aka yi.

"Jinin wadanda aka kashe ba zai je ga banza ba, akwai bukatar zakulo wadanda suka yi wannan aika-aikar don su fuskanci hukuncin abin da suka yi". Sanata Wamakko