Sokoto: Gidajen Mai, 'Yan Kasuwa Da Bankuna Sun Dena Karbar Tsaffin Takardun Naira

Sokoto: Gidajen Mai, 'Yan Kasuwa Da Bankuna Sun Dena Karbar Tsaffin Takardun Naira
 

Wasu masu gidanjen mai, yan kasuwa da kuma bankunan kasuwanci sun kauracewa umarnin kotun koli da kuma shawarwarin hukumomin kasa akan dokar sabon kudi, inda suke cigaba da kin karbar tsohon kudi a Jihar Sokoto. 

Rahotanni daga The Punch sun tabbatar cewa da yawa daga cikin bankunan kasuwanci a jihar ba sa karbar tsohon kudi daga abokan huldar su. 
Wani abokin huldan banki, wanda ya shaidawa majiyar, ya ce: ''Ina banki da safiyar nan don ajiye kudi amma babban abin mamaki, masu karbar kudin sun ki karbar tsofaffin kudin mu. 
''Mun yi kokarin yin magana da shugaban reshen, wanda ya shaida mana cewa babban bankin kasa CBN ya turo da umarnin a daina karbar tsohon kudi. 
''Abin takaici ne hukumomin da ke karkashin gwamnatin tarayya suki bin umarnin da kotu ta ba su, hakan ba daidai bane.'' Sannan, an ruwaito cewa da yawa daga cikin gidajen mai, musamman babban kamfanin mai na kasa NNPC sun ki karbar tsofaffin kudin a hannun abokan hulda. 
Wannan dalilin kamar yadda rahotanni suka bayyana ka iya janyo karuwar yanayin rudanin da ake ciki a jihar. 
Wani mazaunin jihar da ya zanta da wakilin majiyar Legit ya yi Allah wadai da matakin babban bankin kasa CBN da kuma gwamnatin tarayya na rashin sauraren koken talakawa a kasar. 
''Abin da yake shirin faruwa zai iya zama mai muni fiye da zanga-zangar 'End SARS, wanda ya jawowa kasar koma baya. ''Ina shawartar gwamnati da ta dauki matakin da ya dace kafin yan Najeriya su kai bango su fara daukar mataki.'' 
Haka, da yawan yan kasuwa, musamman wanda ke tsofaffin kasuwannin jihar, sun bi sahu wajen kin karbar kudin daga hannun abokan huldar su. 
Wani rahoto daga jihar ya kuma bayyana cewa daya daga cikin masu manyan katafaren kasuwannin zamani da aka fi sani da Alhaji Yaro Gobirawa ya dena karbar tsohon kudi a jihar. Gobirawa, wanda shine tsohon shugaban kungiyar yan kasuwa a jihar, yana daya daga cikin wakilan da suka zauna da babban bankin kasa CBN a jihar da shawo kan matsalar karancin takurdun Naira.