Ban Amince A Nijeriya Ana Shan Litar Man Fetur Miliyan 66 A Kowace Rana Ba----Sarki Sanusi

Ban Amince A Nijeriya Ana Shan Litar Man Fetur Miliyan 66 A Kowace Rana Ba----Sarki Sanusi

 

Wai Shan Man Fetur Muke yi: Sanusi Lamido Yace Ta Yaya Ake Shan Litan Mai Milyan 66 a Rana


Tsohon gwamnan bankin CBN kuma tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, ya bayyana rashin amincewarsa da ikirarin shan man fetur lita miliyan 66 a rana da NNPC tace ana yi a Najeriya. 
Sanusi ya bayyana cewa ta yaya za'a rika shan wannan adadin man fetur kulli-yaumin tun da ba ruwan sha ba ne.
Tsohon Sarkin ya bayyana hakan ne ranar Asabar a taron zuba jarin jihar Kaduna KadInvest7.0, rahoton ChannelsTV. 
"Wai shin shan man fetur muke yi kamar ruwa?" 
"NNPC na fada mana cewa muna shan litar mai milyan 66 a rana. 
Muna sha fiye da Indonesia, Pakistan, Egypt, Cote d’Ivoire, da Kenya." 
"A 2019, litan mai milyan 40 muke shigowa da shi. Yanzu a 2022, lita milyan 66. 
Cikin shekaru uku, mun kara yawan shan mai da kashi 50%. Shin adadinmu ne ya kara yawa? motoci ne suka kara yawa? Ka tambayi kan ka, ta yaya hankali zai dauki wannan."
Sanusi ya cigaba da Alla-wadai da kudin tallafin da ake biya idan yayi kira da a sayar da NNPC kowa ya huta saboda babakere wasu yan tsiraru ke da dukiyar Najeriya.