Muna son a koya mana Sana'a sabanin Bamu tallafi---Masu Laura ta musamman ga Gwamna Ahmad Aliyu

Muna son a koya mana Sana'a sabanin Bamu tallafi---Masu Laura ta musamman ga Gwamna Ahmad Aliyu
Mutane masu lalura ta musamman a jihar Sakkwato sun roki Gwamnan Sokoto Ahmad Aliyu ya samar musu da Shirin koyar da sana'o'in hannu domin ba da tasu gudunmuwa ga cigaban jihar Sakkwato.
Malam Hudu Isa Kebbe ya sanar da haka in da ya bayyana gwamnatin jiha na ba su alawus a wata 6,500.
Isa Kebbe ya bayyana mutane masu lalura na bukatar koyar da su sana'a sabanin kudin da ake ba su don rage fatara.
"Muna son ba da tamu gudunmuwa ga samar da kudin shiga da yanke hukunci a jiha domin Muna da wadan da suka yi karatu Mai zurfi a jiha."