Kansila A  Kebbi Ya  Raba Kayan Abinci Ga 'Yan Gudun Hijira

Kansila A  Kebbi Ya  Raba Kayan Abinci Ga 'Yan Gudun Hijira

 

Daga Abbakar Aleeyu Anache, 

 

Zababben Kansilan Rikoto dake karamar hukumar Zuru a jihar kebbi Honarabul Ayuba Muhammad Rikoto ya Tallafawa yan gudun hijira da kayan abinci domin saukaka musu al'amuran yau da kullum. 

 
Ayuba Rikoto ya ba da wannan tallafi ne a karkashin jagorancin gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu, wannan tallafin ya biyo baya ne ga 'yan gudun hijira dan rage musu radadin da suke fama dashi na rayuwa.
 
Sakamakon fitinar yan bindiga da ya rabasu da garuruwansu, an kaddamar da rabon kayan abincin ne ga yan gudun hijirar da ke Unguwar Rikoto ta saman dutse, inda kowanne ma gidanci ya amfana da shinkafa. 
 
Haka kuma ya yabawa shugaban Karamar hukumar mulki Zuru Hon Bala Mohammed Isah Gajere a bisa yadda yake Kokari wajen tabbatar da jindadi da walwalar yan gudun hijira.
 
Hon Ayuba Muhammad  shi ne  ya jagoranci tawagarsa zuwa wurin kaddamar da rabon kayan abinci ga yan gudun hijirar fiye da 200 da ke zaune a Unguwar Rikoto ta saman dutse da ke cikin garin Zuru suka amfana da tallafin kayan abinci daga Kansilan RIkoto.
 
Ya bada tabbacin cewa gwamnatin jihar Kebbi tana iyakar bakin Kokarin ta wajen ganin yan gudun hijira sun koma gidajensu na asali domin gujewa Iftila'in yan bindiga, da suka addabi wasu yankunan da ke yankin Masarautar Zuru. 
 
A jawabi na godiya sarkin dutsen Rikoto ya yaba kan kokarinsa wajen ganin ya kyautatawa al'umma bisa yadda al'umma suke shan walaha a lokacin gudun hijira, kana kuma ya yabawa gwamnatin jihar kebbi bisa kokarin ta na ganin an samu Kwanciyar hankali da zaman lafiya akan masu tayar da kayar baya. 
 
Yadda aka yi rabon kayan abinci yan gudun hijira sun bayyana farin cikinsu sosai ta yadda Hon Ayuba RIkoto ya ke basu gudunmuwa sosai wajen ganin sun samu abinci ingantanci.