Sabuwar dokar tsaro a Zamfara ta zo daidai da lokaci---Shugaban ƙungiyar 'yan kasuwa

Sabuwar dokar tsaro a Zamfara ta zo daidai da lokaci---Shugaban ƙungiyar 'yan kasuwa

Kungiyar yan kasuwar dake babbar kasuwar Gusau sun yi lale marhaban da sabuwar dokar rufe kasuwan nin mako mako.

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Anyi kira ga mambobin kungiyar yan kasuwa dake babbar kasuwar Gusau dake jihar Zamfara da su kasance masu bin doka da oda, da kuma marawa gwamnati baya domin cimma nasarar dakile ayyukkan yan ta'adda a fadin jihar Zamfara.

Shugaban kwamitin riko na kungiyar Alhaji Bashiru mai manja ne yayi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Gusau dake babban birnin jihar ta Zamfara.

Yace wannan dokar tazo dai dai lokacin da jama'a ke cikin wani mawuyacin halin rashin tsaro, inda ya kara yin kiran dasu tabbatar da dokar da gwamnati ta gindaya masu.

 Shugaban kwamitin rikon wanda kuma shine shugaban kungiyar masu sayar da manja a wannan jihar ya kara da cewa, sun bi wannan dokar kuma ba zasu bude kasuwar Gusau ba, a ranar litinin da jumu'a kamar yanda aka umur cesu.

Alhaji Bashiru , daga nan ya yabawa gwamna Bello Muhammed Matawalle bisa ga kyakkyawan kulawar da yake ba yayan kungiyar su, in ga yace ya gyara babbar kasuwar Gusau, ya kuma samar masu da tallafi domin  su bun kasa kasuwan cin su.

Yace  waccan gwamnatin data gaba ta kwashe shekara takwas bata taka kulawa da matsalar yan kasuwa ba, amma yanzu gashi wannan gwamnatin ta Bello Muhammed Matawalle bata wuce shekara biyu ba, amma ga ta basu kulawa ta musamman.