Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Kebbi Za ta raba man fetur Kyauta ga manoma a  Ramadan

Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Kebbi Za ta raba man fetur Kyauta ga manoma a  Ramadan

Gwamnatin jihar Kebbi karkashin jagorancin Gwamna Nasir Idris ta yi shiri  na musamman domin raba abinci kyauta ga mabukata a lokacin watan Ramadan.

Kwamishina a ma'aikatar Gona ta jihar Kebbi Alhaji Shehu Mu'azu ya sanar da hakan a lokacin gabatar da taron manema labarai na sati-sati a birnin Kebbi Wanda ma'aikatar yada labarai ta shirya. 

Kwamishinan ya ce gwamnati ta tsara yanda za ta raba man fetur kyauta ga manoma domin su yi noman rani an yi haka ne don a saukaka wahalar noma.

Mu'azu Shehu ya zayyano cigaba da gwamnati ta samar a haujin noma in da aka samar tsarin farrfado da aikin noma domin Kebbi ta cigaba da rike kambunta a gefen noman shinkafa a Nijeriya.

Ya sanar da manema labarai gwamnatin jiha ta biya kasonta a cikin shirin RAAMP a shirin za a samar da hanyoyin mota masu tsawon kilo mita 240 don manoma su samu saukin sufuri, gwamnati ta sanya miliyan 350 a shirin.

Bayan manoma dubu 30 dake noman rani na shinkafa da masu noma masara 7500 da masu noma rogo 2000 DA gwamnati ta tallafama.

Kwamishina ya ce gwamnati ta Gina karamin wurin noma na zamani a karamar hukumar Argungu da Fakai a garin Mahuta.