Harin 'yan bindiga a makarantar sojoji ta  Kaduna sun kashe soja 2 da sace Maijo guda

Harin 'yan bindiga a makarantar sojoji ta  Kaduna sun kashe soja 2 da sace Maijo guda
Harin 'yan bindiga a makarantar sojoji ta  Kaduna sun kashe soja 2 da sace Maijo guda
Rahotanni sun nuna cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari Makarantar Sojoji ta Nigeria Defence Academy, NDA, da ke birnin Kaduna.
Wasu bayanai sun tabbatar da cewa an kai harin ne a daren jiya in da aka sace soja guda aka kashe biyu.
Sanarwar da mai magana da yawun Makarantar Sojojin Bashir Muhammad Jajira ya fitar daga bisani ta tabbatar da kai harin.
Ya ce 'yan bindigar sun shiga bangaren gidaje na Makarantar inda suka kai hari lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami'ansu biyu sannan aka sace guda daya.
Amma bai bayyana mutanen da aka kashe ba, da kuma wanda aka sace. Sai dai wasu bayanai da BBC Hausa ta samu sun tabbatar da cewa an kashe "Lt Cdr Wulah da Flt Lt CM Okoronwo" sannan aka sace Manjo Datong.
"Al'ummar NDA da 'yan makarantar horas da sojoji suna cikin koshin lafiya a Makarantar. Muna tabbatar wa jama'a cewa za a kamo wadannan 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba nan gaba kadan, sannan a ceto jami'in da aka sace," a cewar Bashir Muhammad Jajira.
Ya kara da cewa hukumomin Makarantar da hadin gwiwar Runduna Ta Daya ta Sojin Kasan Najerriya da Rundunar Horas da Sojin Sam da ma sauran jami'an tsaro da ke Kaduna sun soma bin bayan 'yan bindigar da zummar far musu da kuma ceto mutumin da aka sace.
Aiyukkan maharan na ƙara yawa a waɗan nan jihohin ba ƙakƙautawa.