PDP za ta bayar da takarar shugaban ƙasa ga yankin Arewa
Akwai matuƙar tsammanin jam'iyar PDP za ta bayar da takarar shugaban ƙasa a ɓangaren Arewacin Nijeriya a zaɓen 2023 in da za ta kai matsayin shugaban jam'iya a gefen kudu.
A lokacin taron shugabannin jam'iyar a ƙarshen sati sun sanar da cewa za su faɗi yanda karɓa-karɓar za ta kasance a zaman da za a yi ran 9 ga Satumban 2021.
Wannan ya zo ne kan faɗi tashin jagororin siyasar jam'iyar ke yi wanda yakai ga sanya 30 da 31 na Okotoba za a yi babban taron jam'iyar.
Zaɓen shugabannin jam'iyar zai cigaba duk da rigimar shari'ar da ake yi a kotuna.
Yankin Arewa maso Yamma har yanzu bai da zaɓaɓɓin shugabanni tun sanda aka shirya zaɓe bai yiwu ba kan rigimar Tambuwal da Kwankwaso abin jira a gani za a yi zaɓen kafin babban taro ko sai bayan taron.
managarciya